Gwamna Ganduje yana Saudia domin gudanar da ibadar Umrah

0
283

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje yana kasa mai tsarki shida iyalansa domin gudanar da ibadar Umrah tare da godewa Allah bisa ni’imomin da ya yi masa.

Hoto Na Farko: gwamna Ganduje yana can kasa mai tsarki shida iyalansa suna ibadar su cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.

Hoto Na Biyu: Mai girma mataimakin gwamna ne Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilci gwamna Ganduje wurin duba Alh. Yahaya Bagobiri daraktan yakin neman zaben Alh. Atiku Abubakar wanda yake kwance a Asibiti ba bu lafiya.

Hoto Na Uku: Mai girma Sanatan Kano ta tsakiya ne Malam Dakta Ibrahim Shekarau shima ya ziyarci Asibiti domin duba Alh. Yahaya Bagobiri bisa rashin lafiya. Wanda yake Asubitin Malam Aminu Kano yanzu haka muna fatan Allah ya ba shi lafiya.

Amman da yake wasu ‘yan adawar siyasa sun koma siyasar hauka shi ne suke yadawa cewar gwamna Ganduje yana kwance a Asibiti ba bu lafiya, duk mutane suna mantawa cewar Allah shi ne mai kowa mai komai kuma mai yadda yaso ganin damarsa ce ya bawa kowa lafiya kuma ya hana kowa lafiyar har kai da kayi wancan furuci dani da na yi wannan maganar idan yaga dama sai Ganduje ya rasa lafiya wannan ikon sa ne Allah Ta’ala amman saboda siyasa ta shirme ka ringa nemawa wani bawa larura ko musifa bayan Allah shi ne mai yin komai.

Wannan tunatarwa ce ga ‘yan uwa kowa da kowa kar mu manta cewar rayuwa fa ba dawwamammiya ba ce, kuma ita siyasa a nan doron duniya ake yin ta ake barinta shi yasa ake son mutane su ringa yin siyasa mai tsafta ba tare da zafafawa ba ko cin mutuncin wani ko wata ba, ga duk wanda yasan siyasa an doratane akan kalamai na hikima da ilimi gudun samun matsala a nan duniya da kuma lahira, domin shi ubangiji ba bu ruwan sa da siyasar ka aikin da kayi za a duba da kalaman da ka yi kurum zai yi aiki da shi, A wannan lokacin da muke ciki siyasa dole ce kuma ita sai da adawa amman ya kamata mu ringa tsarkake bakunan mu gudun abun da zai same mu ranar gobe kiyama akwai ranar da aka tambiyi bawa abun da ya aikata, kuma aikin alkairi ko sharri yana yin kwana ya dawowa mai shi.

Allah ya kare mu ya kiyaye harasan mu akan fadin ba daidai ba akan kowane dan adam, Allah ya bawa shugabannin mu ikon aikata daidai garemu ya kuma bamu ikon yi musu biyayya kamar yadda Allah Ta’ala ya tsara mana.

  1. Daga Anas saminu Ja’in

Leave a Reply