MAFITA GA MATAN AURE DA SUKE ZINA KO KARUWANCI (kashe na 1)

1
1162

Daga Datti Assalafiy

Abu na farko da zamu tattauna akan abinda yake jefa matan aure zuwa ga aikata zina shine “rashin samun gamsuwar jima’i daga mazajen su na aure”

Ma’aurata zasu fi kowa fahimtar wannan tattaunawa, babu shakka duk matar da bata samun isasshen gamsuwa a gurin mijinta to rayuwarta tana cikin hatsari, domin tana fuskantar barazana na fadawa tarkon zina, kalilan ne daga cikinsu masu hakuri da tsoron Allah suke iya jurewa su tabbata cikin hakuri da mazajensu.

Duk magidanci da yake tare da matarshi na aure ya kamata ya karanci karfin sha’awar matarshi, sai yayi wa kanshi tanadin da zai iya gamsar da ita ta hanyar neman magani ko shawarwari daga masana ilmin jima’i.

Mazajen aure da suke yin dogon tafiya su dauki lokaci basa tare da matansu na aure; matansu na daga cikin wadanda suke iya zuwa neman mazan banza da zasu dinga biya musu bukata, akwai wani shekara a wani gari an taba kama wata mata da daddare ana zina da ita a cikin mota, abin takaici matar a shekarun haihuwa ta kusa haifan abokin lalatan nata, da ana mata tambayoyi cewa tayi laifin mijin ta ne, ya kasance mai yawan tafiya kuma zai dauki lokaci bai dawo ba.

Cutar basir da take rage wa maza karfi, wannan yana daga cikin abinda yake cutar da maza, an saka lalaci ba’a motsa jiki, babu wani maganin basir da ya wuce motsa jiki, duk mutumin da yake motsa jiki to ba basir ba hatta kananun cututtuka zaiyi wahala su shafe shi balle har su rage masa karfin da zai kasa gamsar da iyali.

Game da illar cutar basir da rashin motsa jiki, mai neman karin bayani yaje tambayi karuwa mai zaman kanta wacce take mu’amala da maza iri-iri, karuwa zata tabbatar maka cewa tabbas akwai banbanci wajen samun gamsuwar jima’i tsakanin namijin da yake motsa jiki da wanda bai motsa jiki.

Shan kwayoyi masu kara karfin jima’i, muna cikin wani zamani, matashi da zaran yayi aure sai masu tallen magani su fara binshi har gida suna cewa ga wannan maganin raini ne, kada amarya ta renaka, kar ka bawa abokanka kunya, daga haka ne ake fara renon wasu mazan aure da shan kwayoyin kara karfin jima’i, likitoci sunce duk matashin da ya reni kanshi da shan kwayoyin jima’i kanshi yake cutarwa.

A duk lokacin da matashi ya lazimci hadiyar kwayoyin kara karfin jima’i, jijiyoyin da suke tayar masa da gabanshi zai kasance suna aiki sosai fiye da yadda Allah Ya tsara suyi aiki, kuma ba za’a dauki lokaci mai tsawo ba jijiyoyin sun fara gajiya saboda shan kwayoyi, har ya zamto cewa matashi magidanci sha’awar sa ba za ta motsa ba sai yasha kwaya, yana fara riskar shekarun tsufa kuma shikenan jijiyon sun mutu, yanaji yana gani ga matar ba zai iya mata komai ba, daga nan idan ba mai tsoron Allah bace sai ta fara neman wanda zai gamsar da ita a waje.

Wannan yana daga cikin illar shan kwayoyin da suke kara karfin jima’i ga maza, matashi kayi hakuri da shan kwayoyi, ka rungumi motsa jiki kadai ya wadatar da kai, ka bari idan ka riski shekarun tsufa sai ka fara shan kwayoyi karin karfi, musamman tuzurai da ba suyi aure ba su kiyaye wannan shawara.

Wannan shine bayani a takaici akan rashin samun gamsuwar jima’i daga mazajen aure da yakan jefa matan aure zuwa ga zina.
Insha Allahu a rubutu na gaba zamu dauki maudu’i na biyu mu tattauna.

Allah Ya yafe mana, Ya shiryar damu, Ya karemu daga sabon Allah Amin.

1 COMMENT

  1. Macha allah wanan bayani yana gamsarwa ,allah ya bada lada bisa ga gudumuwar da kuke bayarwa malam wajen giyara da nema ma al’umar annabi mohamed saw mafita da fadakarwa .

Leave a Reply