KU RIKE ALKUR’ANI KU KARANTA SHI DARE DA RANA – Mai Martaba Sarkin Kano

0
274

“Ku rike alkur’ani, ku karanta shi dare da rana, shi ne haske a cikin kowane duhu kuma shi ne waraka daga dukkan al’amura.

Kar ayi sauka a ce an jingine karatun, a yi ta muraja’a, bayan daukakar da kuka samu a wajen Allah a rayuwarku ta duniya ma ta ko wanne fanni za ku samu haske a ciki, ko da karatun boko mutum yake in dai yana hadawa da karanta alkur’ani mai tsarki Allah zai ba shi kwakwalwa da fahimta don kur’ani ba abin wasa ba ne duk wanda ya rike shi to ya yiwa kansa garkuwa”

Mai Martaba Sarkin Kano Muhammad Sanusi II CON yayin da halarci Saukar Alkur’ani Mai Girma wadda aka yi a makarantar Ma’ahad Sheikh Abubakar Nagoggo dake Unguwar Sarari, Koki.

Daga Sa’adatu Baba Ahmad

Leave a Reply