SAI YAUSHE ‘YAN AREWA ZA SU DENA ‘KORAFI A NAGERIA ?

0
234

Daga Garba Tela Hadejia

bbas, Allah ya yi wa yankin Arewa dumbin arziki da tarin ni’imomi wadanda ba za su taba kidayuwa ko misaltuwa ba. Misali:

Allah ya yi mana arzikin mutane masu tarin ilimi na addini da na zamani kuma gogaggu a fagen wayewa da sanin rayuwa.

Sai dai kuma, duk da irin wannan tarin masana da Allah ya yi mana, amma abin takaici kullum ba mu da aiki sai ‘korafi kan Shugabannin da su ke mulkar ‘kasar gaba ‘daya.

A kullum zarginsu mu ke su na fifita kudu akan Arewa, amma kuma mun manta da cewar: mutanen Kudu kafin su yi wa duk wani Shugaba ‘korafi ko raki, sai sun mika masa jadawalin muradu da bukatunsu cikin maganar fatar baki da kuma aike masa da rubutaccen sako ta hanyar Shugabanni da manyansu. Har sai in Shugaban ‘kasar ya ‘ki cika musu muradunsu ne tukunna su ke fitowa su yi ‘korafi da irin yaren da wannan Shugaban ‘kasa zai sauraresu.

Mu kuma ‘yan Arewa ba ma iya zama mu tsara jadawalin bukatun da mu ke da su kan kowanne Shugaban ‘kasa, har sai mun ga an yi wa ‘yan Kudu wani abu na cigaba tukunna mu fito mu fara raki da ‘korafin an ‘ki a yi mana kaza da kaza. Alhali kuwa mun bar abin tun a baya mun ‘ki mu isar da bukatunmu gare shi ta hanyar Shugabanni da manyanmu.

Tabbas ya kamata jama’ar Arewa su gane, matsayin Shugaban ‘kasa ‘danku ba shi zai ba ku lasisin samun komai daga gare shi ba, dole sai kun hada kanku kun nema kun bi sawu tukunna.

Leave a Reply