DA NI NE SARKIN KANO:-

0
533

Daga Garba Tesa Hadejia

Tabbas, duk wanda ya ke biye da akasarin zantuka da kalaman mai martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sunusi na biyu, zai fahimci mutum ne da ke da halayyar ‘kin jinin tallace-tallace da barace-barace da kuma jahilci da zaman kara zube cikin al’ummar Arewa.

Haka zalika, mai martaba mutum ne da ya ‘ki jinin keta hakkin bil’adama da kuma zaluntar mata gami da ‘kin jinin mutuwar aure barkatai a yankin Arewa.

Kenan a dunkule za mu iya cewa mai martaba mutum ne da ya damu da damuwar al’ummar Arewa ya ke kuma takaicin halin da Arewa ta samu kanta a yau na koma bayan Ilimi da tattalin arziki da kuma kiwon lafiya.

Haka zalika, al’umma sun shaida mai martaba Sarki mutum ne mai tarin Ilimi na addini da na zamani, kuma a ko’ina zai amsa sunan jagora domin mutum ne mai juriya da jajircewa gami da damuwa da damuwar al’ummarsa.

A fahimtata, sai na ke ganin da ni ne mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi Na Biyu, zan kame bakina daga furta duk wasu matsaloli da su ka shafi Arewa a baynar jama’a.

A madadin hakan zan maida hankali ne wajen samun lokaci da tsara manhaja da jadawalin matsalolin Arewa da kuma hanyoyin da za abi a magance su.

Daga cikin tsarin da zan bijiro da shi: zan tsara yadda zan tuntubi sauran takwarorina sarakunan gargajiya da kuma rawar da za su taka su da hakimai da dagatai da masu unguwanni.

Zan kuma yi tsarin da za mu hada ‘karfi da ‘karfe da ‘yan Siyasar Arewa ba tare da la’akari da bambancin jam’iyyar Siyasa ba.

Idan na kammala da wannan tsari, zan tunkari mai martaba Sarkin Sokoto, a matsayinsa na jagoran Daular Usmaniyya kuma Shugaban duk wani Sarki a Arewa, zan ba je masa komai a faifai na daga irin tsarin da na yi kan yadda za a magance matsalolin Arewa.

Zan kuma bayyana masa cewa zan ziyarci duk wani Sarki a fadarsa za mu tattauna wadannan batutuwa da shi.

Sannan kuma daga baya sai na tsara yadda za mu kira taron
Sarakunan Arewa gaba ‘daya, mu tattauna a dunkule mu tsayar da magana da murya guda kan duk wata matsala da ke addabar Arewa.

Daga nan kuma sai mu kira taro da ‘yan Siyasarmu na Arewa gaba ‘daya da sarakunan ta yadda a nan ma za mu yi magana da murya guda kan komai da ya shafi Arewa.

Idan mun gama da wannan, sai mu kuma zakulo manyan masana da ‘yan Boko da ‘yan Kasuwa da manyan Malamai da Attajirai ‘yan Arewa mu ‘kara shawartawa da juna mu kuma samu hadin kai a tsakani.

Kenan, Sarakuna sun shigo, ‘yan Siyasa sun shigo, attajirai da malamai da ‘yan Boko da ‘yan Kasuwa na Arewa gaba ‘daya kowa ya shigo. Abu na gaba kuma sai mu shiga aiki gadan-gadan tunda mun samu ‘karfi na hadin-kai da yin magana da murya guda.

Wannan hadaka, za ta kasance za ta rika magana da murya guda kan duk abin da ya shafi Arewa ba tare da la’akari da bambancin Siyasa ko wani ra’ayi ba. Arewa kawai za mu sanya a gaba domin abin da ya kamata mu yi za mu hada ‘karfi da ‘karfe mu yi.

Hakkin Arewa kuwa ba a gwamnatin tarayya ba, ko a majalissar ‘dinkin Duniya ne za mu je mu karbo.

Me ya sa na ce da ni ne Sarkin Kano ? Na zabi Sarkin Kano Malam Sunusi Lamido Sunusi ne duba da yadda na fahimci shi ne Sarki ‘daya tilo da ba ya fargabar bayyana abin da ya dame shi. Kuma mutum ne da wadannan matsaloli na Arewa su ke ci wa tuwo a ‘kwarya. Haka zalika, mutum ne mai Ilimi na addini da na zamani da kuma gogewa da rayuwa.

Wane dalili ne ya sanya na ce a yi hadakar Sarakuna da ‘yan Siyasa da Malamai da masu kudi da masana da ‘yan Boko kan matsalolin Arewa ? Dalili shi ne duk al’ummar da ka ga ta cigaba a Duniya to sai ta hada kanta ta kuma kauda sabani da bambance-bambancen da ke tsakaninsu.

Haka zalika kowane rukuni na wadannan mutane akwai rawar da zai taka. Wato akwai hurumin da ya ke na ‘yan Siyasa ne, akwai rawar da sarakuna ne za su taka ta akwai rawar da ta ke ta ‘yan Boko ce da Masana wata rawar kuma ta Malamai ce da ta attajirai. Ya yin da kuma wata rawar hadakarsu gaba ‘daya ta ke bukata.

Leave a Reply