Fim Din Hausa Ko Fim A Harshen Hausa?

0
265

Daga Bukar Ali

Hakika abubuwan da suka faru a tsakankanin nan sun janyo ce-ce-ku-ce da dama dangane da fina-finan Hausa da kuma masu shirya su. Dama can an dade ana yi wa masu sana’ar kallon mutane masu karancin tarbiya da kuma mutunci. Abu na farko da ya fara tabbatar da hakan shi ne wata barna da ta bayyana shekarun baya inda bidiyo ya bullo na wata yar fim tana aikata fasadi da wani mutum. Wannan ya zubar wa sana’ar mutunci sosai, inda har wasu masu mutunci irinsu Sule Koki suka fita a harkar.

Inda Allah ya rage ma aya zaki shi ne kasancewar lokacin ayyukan ‘Social Media’ ba su zama ruwan dare ba; da abin ya yi muni sosai.

To a kwanakin nan sai gashi muna ganin irin yadda masu wannan sana’a ta wasan kwaikwayo suke jifan junansu da miyagun zarge-zarge na fasikanci wanda ko ya ka so kyautata masu zato ka san akwai kamshin gaskiya a ciki. Hakika da yawa ba mu yi mamakin irin wannan aika-aika ba dake faruwa a masa’antar tunda dama mutane ne masu dauke da alamomin tambaya a tare dasu.

To shi wannan fina-finai da ake kira ‘Hausa Films’, wato fim din Hausa haka suke? A ma’ana, fim din Hausa na nufin fim da akayi shi da harshen Hausa kuma yake tafiya da tsari da kuma al’ada irin na bahaushe. Fina-finan da muke gani a yanzu kuwa babu kunya, babu dattako da tsantseni a cikin su.

Da wannan nake ganin cewa abin da ake yi yanzu saidai mu kira shi da ‘fim a harshen Hausa’ kamar yadda inyamurai da Yarbawa ke yin fina-finai a harshen turanci ba tareda an alakanta fim dinsu da Turawa ba. Suma a daina alakanta iskantakunsu da Hausawa.

Leave a Reply