ME SHUGABA MUHAMMADU BUHARI ZAI JE YI A ‘KASAR BIRTANIYA ?

0
315

Daga Garba Tela Hadejia

Cikin daren jiya, fadar Shugaban ‘kasar Nageriya, Janar Muhammadu Buhari, ta fidda wata sanarwar ta bakin Malam Garba Shehu, mai magana da yawun Shugaba ‘kasar, inda su ka labarta cewa: a yau Shugaban ‘kasar zai kai wata ziyara ta musamman ‘kasar Birtaniya Bayan ya kammala ziyarar aiki a Jihar Borno.

Kuma ana sa ran ba zai dawo ba har sai ya shafe tsawon kwanaki a ‘kalla goma (10) kafin ya dawo gida Nageriya.

Kamar yadda jama’a su ke sane, Shugaba Muhammadu Buhari a baya ya yi fama da matsananciyar rashin lafiya wacce ta haifar masa da shafe tsawon watanni ya na zaman jinya a ‘kasar ta Birtaniya.

Kuma bayan da aka sallamo shi, a ranar da ya dawo ya zanta da manema labarai ya shaida musu cewa ba shakka ya yi matsananciyar rashin lafiyar da bai taba yin irinta ba a rayuwarsa. Kuma Allah ya ba shi lafiya, amma lokaci bayan lokaci zai rika zuwa ganin Likitansa a can.

Bugu da ‘kari, a baya Shugaba Buhari ya amsa wata gayyata ta Shugaban ‘kasar Amurka Donald J. Trump zuwa ‘kasar Amurka, amma bayan da ya dawo sai jirginsa ya yada zango a birnin Landan wanda hakan ya jawo cece-ku-ce a ‘kasa tare da taraddadin ‘koshin lafiyar Shugaban.

Haka dai ake cigaba da kasancewa cikin cece-ku-ce da guna-guni gami da raba ‘daya biyu game da ‘koshin lafiyar Shugaba Buhari a duk lokacin da ‘yan ‘kasa su ka ji labarin zai ziyarci ‘kasar Birtaniya.

Saboda sun san ya taba zaman jinya acan na tsawon lokaci, kana kuma ba shi da wata ‘kasa da ya ke zuwa neman magani fiye da Birtaniya.

To sai kuma ga shi a yanzu fadar Shugaban ‘kasa ta sake fidda sanarwar cewa Shugaba ‘kasa zai ziyarci Birtaniya kuma ziyara ce ta ‘kashin kansa.

Sai dai gwamnatin ba ta bayyana hakikanin abin da zai kai Shugaba Buhari Landan ‘din ba a wannan lokaci. Amma saboda ma kada ‘yan adawa da sauran al’ummar ‘kasa su yi zaton cewa rashin lafiya ce za ta fidda Shugaban ‘kasar, sai fadar Shugaban ‘kasa ta yi sauri ta yi wa tufkar hanci ta hanyar bayyana cewa:

A wannan ziyara ta kwanaki goma da Shugaban ‘kasa zai kai Birtaniya, be bar wa matemakinsa Farfesa Yemi Osinbanjo rikon ‘kasar ba, hasali ma ya na daga can ‘kasar ta Birtaniyan zai cigaba da gudanar da Shugabancin ‘kasar har zuwa tsawon kwanakin da zai shafe.

Saboda al’umma su fita daga shakku, su kuma gamsu da lallai Shugaba Buhari cikin ‘koshin lafiya ya ke tunda ga shi bai bar ‘kasar a hannun matemakinsa ba, kuma har ma zai na gudanar da aikin Ofishinsa na Shugaban ‘kasa daga can birnin na Landan.

-Garba Tela Hadejia
Alhamis, 25/4/2019.

Leave a Reply