Yau Ce Ranar Zazzabin Cizon Sauro Ta Duniya

0
217

Daga Anas Saminu Ja’en

A WANI BINCIKE: Ko ka san cewa kimanin mutane 435,000 suka mutu sakamakon zazzabin ciwon sauro a shekarar 2017 kawai a faɗin duniya? Ana iya kare musamman yara da mata masu juna biyu daga zazzabin cizon sauro idan muka tsabtace muhallan mu kuma muka yi amfani da gidan sauro mai magani yayin kwanciya.

Kuma zazzabin cizon sauro na iya ratsa kwakwalwar yara har ya yiwa kwakwalwar illa da ake cewa (Cerebral Malaria) a turancin likita, Matsalolin da kan biyo bayan ratsawar zazzabin cizon sauro zuwa kwakwalwa ga yaran da suka samu tsallakewa ba su mutu ba, sun hada da dakushewar aikin kwakwalwa, kagewa ko rirriƙewar gabobi, da dai sauransu.

Likitocin na taka muhimmiyar rawa a jinyar yaran da suka kamu da zazzabin cizon sauro har zuwa kwakwalwa da suka zo da matsalar rirriƙewar gabobi, kuma binciken da likitoci suka yi sun gano cewar a kowanne minti biyu sai yaro ya mutu saboda zazzabin cizon sauro?

Mu yaki sauro a yau kafin ya yakemu gobe, Allah ya bamu lafiya ya kare mu da zazzabin cizon sauro.

Leave a Reply