GWAMNATIN NAJERIYA TA WARE KUDI KIMANIN BILYAN HAMSIN DA BIYU (N52bn) DOMIN KULA DA IYAKOKIN KASAR NAN.

0
169

Daga Mubarak Musa Al-mubarak

Da yake Tattaunawa da Yan jarida bayan Kammala zartar da wannan Kudirin a wannan rana ta Alhamis, Ministan Cikin gida Abdurrahman Bello Dambazau yace Kwangilar zata shafi kula da saka ido a kan Iyakokin(Borders) kasar nan guda 86 tare da wasu barayin Hanyoyin da ake shigo da kayayyaki ba bisa ka’ida ba guda 1,400.

Dambazau ya Kara da cewa akwai wani tsari da za’a Sanya kananun jirage da zasu ringa shawagi a dukkanin Iyakokin ta hanyar yin aiki tare da hukumar Sojin sama ta kasa. Baya ga haka za’a Karfafawa Hukumar Shige da fice ta kasa Wanda zasu yi aiki kafada da kafada da hukumar Kwastom domin Kara karfafa tsarin Iyakokin Kasar.

Wannan kwantaragi ne da zai kai har tsawon Shekaru 2 masu zuwa; A Cesar Minista Dambazau.

Leave a Reply