INA MAKOMAR TSARON AREWACIN NIGERIA TSAKANIN GWAMNATIN SHUGABA BUHARI DA GWAMNATIN MACIYIN AMANA JONATHAN ?

0
926

Daga Datti Assalafiy

A rubutun da na gabatar jiya, nayi bayanin cewa siyasar demokaradiyya a Nigeria tana daf da kafa tarihi insha Allah, a karon farko za’a samu:

Shugaban kasa Musulmi
Shugaban majalisar dattawa musulmi
Shugaban majalisar wakilai musulmi
Shugaban ‘yan sanda musulmi
Shugaban sojojin kasa musulmi
Shugaban sojojin sama musulmi
Shugaban hukumar Custom musulmi
Shugaban hukumar DSS musulmi
Shugaban hukumar leken asiri (NIA) musulmi
Shugaban gidan yari musulmi
Shugaban Civil Defence musulmi
Shugaban NITDA musulmu
Shugaban EFCC musulmi
Da sauransu wadanda suke musulmai.

Wadannan bayanai da na zayyano wasu sunyi zazzafan suka, sukace duk tarin wadannan shugabanni Musulmai amma basu tsinanawa musulunci da Musulmai komai ba musamman a yankin Arewa, wasu sunce gwamma Gwamnatin Jonathan akan na shugaba Buhari.

Wato abin takaici ne matuka yadda har muka kasance masu saurin mantuwa akan tashin hankalin da yankin arewa ya shiga a gwamnatin Jonathan, a lokacin ne fa shugaban Boko Haram Abubakar Shekau yake cika bakin cewa shi fa duniya yazo yaka ba Nigeria ba, kawai saboda Jonathan ya kyaleshi yana cin karensa babu babbaka, amma yanzu Shekau yayi shiri tsit kakeji kamar baya raye.

Inda ace Jonathan ya zarce har zuwa yanzu da yanzu sun mayar da yankin Arewa ya koma tamkar Somalia, da zaben ma ba za’ayi ba saboda tashin hankali, sai dai kawai su daura wanda sukaga dama a cigaba da rusa arewa, Boko Haram kwangilace da manufa aka kawo don a ruguje arewacin Nigeria.

Ku tuna da irin cin kashi da wulakancin da aka mana, ku tuna da yadda aka hanamu sallah a jam’i saboda ana tayar da bama-bamai, ku tuna a lokacin da ake shiga gidan aure na musulmai wai ana binciken bomb, ku tuna da lokacin da ake yiwa kallon masu siffar addini a matsayin ‘yan ta’adda, a dole kawai sai an dusashe hasken musulunci a Arewan Nigeria.

Wadannan shugabannin namu musulmai da muke zagi wallahi albarkacinsu muke ci, Allah Ya bamu su a matsayin sanadi suka tare mana babbar musifa da bala’i.

Wasu suna sukar shugaba Buhari saboda matsalar garkuwa da mutane da ya addabi jihar Zamfara da sauran gurare, duk wanda yake neman gaskiya yasan cewa ba’a gwamnatin shugaba Buhari aka fara samun wannan masifar ba, shugaba Buhari ya gaje ta daga gwamnatin Jonathan, dukkan masu bincike da sharhi akan tsaron Nigeria sun tabbatar da cewa akwai alaka na kungiyoyin ta’addanci da kungiyoyin masu garkuwa da mutane a jihar Zamfara, Ahmad Salkida ‘dan jaridar da yake da alaka da Boko Haram ya tabbatar da wannan.

Sannan wannan matsala na sace mutane akwai hannun wasu manyan ‘yan siyasa da manyan sarakunan gargajiya kamar yadda Ministan Tsaro ya bayyana, kuma duk wanda ya bibiya hanyar da akabi aka iza wutar rikicin masu sace mutane a Zamfara da irin manyan kayan yaki da yake hannunsu to zai fahimci cewa abune shiryayye.

Kuma inda ace a gwamnatin Jonathan ake matsalar Zamfara sai yafi haka munana, tunda yayi akan matsalar Boko Haram mun gani.

Allah Ka taimaki shgaba Buhari Ka bashi nasaran magance mana dukkan matsalar tsaro a arewa da Nigeria.

Leave a Reply