Misali, babu wani gwamna mai ci a yanzu da zai iya jure kalaman ‘batanci daga wani tsohon gwamna ba tare da ya ‘dauki matakin ramuwar gayya ko maida martani da baki ba.

0
434

Daga Bashir Abdullahi El-Bash

A iya Jihar Kano kadai ba, bincike ya tabbatar da cewa Gwamna Ganduje ya fi akasarin Gwamnonin Nageriya hakuri da juriya.

Misali, babu wani gwamna mai ci a yanzu da zai iya jure kalaman ‘batanci daga wani tsohon gwamna ba tare da ya ‘dauki matakin ramuwar gayya ko maida martani da baki ba.

Sai Gwamna Ganduje, duba da yadda ya hadiye dukkan wani bacin-rai da kalaman batanci daga tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Kwankwaso.

Duk kuwa da cewar Gwamna Ganduje ya san duk wani nakasu da gazawar Kwankwaso a Siyasa da rayuwa ma gaba daya, duba da yadda su ka jima tare har ya yi masa matemakin gwamna tsawon shekara takwas.

Amma Gwamna Ganduje bai taba fitowa kafafen watsa labarai ko duk wani wurin taro ya aibata shi ba, kamar yadda shi Kwankwason ya ke yi masa.

Wani abu da zai ‘kara tabbatar maka da cewa gwamna Ganduje ya kai duk inda ya kai wajen hakuri, a baya da Kwankwaso ya matsa masa da lakabin mijin hajiya, sai Gwamna Ganduje ya maida martani da cewa shi fa ya na son matarsa, kuma ba zai aibata iyalin Kwankwaso ba domin ya na ganin kimarsu ya na kuma girmama mata.

Ba shakka, ko a iya nan aka tsaya, Gwamna Ganduje ya kai a kira shi da “Damo Sarkin Hakuri”.

Leave a Reply