WASIKA ZUWA GA SHUGABAN ‘KASA (2):-

0
513

Daga Garba Tela Hadejia

Cikin ladab da biyayya gami da girmamawa a gare ka ya mai girma Shugaban ‘kasar tarayyar Mageriya, Alhaji Muhammadu Buhari (GCFR). Assalamu Alaikum.

Ya mai girma Shugaban ‘kasa, na zabi rubuto maka wannan wasika a daidai wannan lokaci da ka ke ‘kasar Birtaniya.

Domin ina kyautata zaton za ka fi samun cikakken lokaci na yi wa sakon nawa duba na tsanaki ba kamar a Nageriya ba inda shidindimu da ayyuka su ka yi maka yawa.

Ya mai girma Shugaban ‘kasa, Talauci ya yi wa al’ummar ‘kasarka katutu. Wadanda su ka fi ‘karfin cin abinci sau uku, yanzu da ‘kyar su ke iya samu su ci sau ‘daya zuwa sau biyu.

Wadanda su ka fi ‘karfin bukatunsu guda goma, yanzu da ‘kyar su ke iya fin ‘karfin bukatunsu uku zuwa biyar.

Masu aikin yi da sana’o’i ma kasuwar ta zama sai a hankali, mai fita ya yi cinikin dubu ‘daya yanzu da ‘kyar ya ke iya yin cinikin ‘dari biyu zuwa ‘dari biyar. Saboda babu kudi a hannun mutane.

Ya mai girma Shugaban ‘kasa, ‘dumbin al’umma Matasa su na nan jifge a ‘kasa babu aikin yi sai zaman ‘kwararo. Na gwamnatin ya ‘ki samuwa, na kamfanonin ma ya ‘ki samuwa, ba su kuma da jarin da za su iya fara sana’a ko ya take.

Ya mai girma Shugaban ‘kasa, a baya mutane da dama sun fi ‘karfin bukatunsu har ma da na wasunsu, amma yanzu nasun ma da ‘kyar da fama su ke iya biya.

Ya mai girma Shugaban ‘kasa, a matsayinmu na magoya bayanka, kuma masoyanka na hakika, kana kuma wakilan al’umma talakawanka, ya zama wajibi mu sanar da kai gaskiyar halin da talakawanka su ke ciki.

Ya mai girma Shugaban ‘kasa, fatanmu ka bijiro da tsare-tsaren da za su taimaka wajen sama musu saukin rayuwa. Saboda kai Allah ya damkawa amanarsu. Kuma za ka zama abin tambaya da tuhuma ranar gobe ‘kiyama idan talakanka ‘kwaya ‘daya tak! Ya kwana da yunwa.

Ya mai girma Shugaban ‘kasa, duk yadda za a kwatanta maka zurfin ramin talaucin da al’umma su ka fada a gwamnatinka abin ya wuce nan. Ba za ka fahimci girman matsalar ba sai ka na shiga cikinsu. Mu kuma mu ne mu ke zama da al’umma mun kuma san halin ‘kuncin da su ke ciki.

Kuma kamar yadda na taba fada cikin wani rubutuna da ya gabata, ba shakka Talakawa sun yi maka uzuri irin uzurin da ba kowane Shugaba za su iya yi wa irinsa ba a ‘kasar nan. Amma saboda ‘kauna da kuma kyautata zato a gare ka, su ke cigaba da zaman hakuri cikin talauci.

Ya mai girma Shugaban ‘kasa, talaucin nan da al’umma su ke ciki, ba makawa shi ke ‘kara rura wutar sace-sace da fashi da makami da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa. Saboda duk lokacin da ‘dan adam ya rasa abin yi, to fa duk mugun aikin da zuciyarsa ta ‘kawata masa zai iya fadawa.

Ya mai girma Shugaban ‘kasa, hakika, ba a gwamnatinka kadai Allah ya fara saukwar da jarrabawar talauci da yunwa ga al’umma ba. Hatta a gwamnatin Khalifofi bayan shudewar Manzon Allah (S.A.W). Allah ya saukwar da wannan jarrabawa.

Amma hakan bai sanya Shugabannin sun nade hannunsu ba. Amfani su ka yi da damar su wajen samar da tsare-tsaren da su ka taimaka wajen fidda al’umma daga ‘kuncin da su ke ciki.

Ya mai girma Shugaban ‘kasa, mun sani Gwamnatinka ta samar da tsare-tsaren rage radadin talauci kamar: ba da tallafin naira dubu biyar-biyar ga masu ‘karamin ‘karfi ko gajiyayyu da kuma ba da tallafin jarin naira dubu goma-goma cikin shirin (TradeMony) da kuma samar da ayyukan yi ga matasa cikin shirin (N-Power). Kuma Alhamdulillah! Shirye-shiryen sun yi tasiri.

Sai dai akwai bukatar Gwamnati ta ‘kara ‘kaimi cikin hanzari ta sake fitar da tsare-tsaren da za su taimaka wajen rage farashin kayan masarufi da kuma wadata matasa da ayyukan yi cikin aikin gwamnati da kuma ba da tallafin jari ga masu sha’awar gudanar da kasuwanci da sana’o’i.

Ya mai girma Shugaban ‘kasa, ba shakka talakawanka da su ka tsaya kai da fata a bayanka tun daga (2003) har zuwa yau, su na cikin wani hali na tagayyara, (yunwa da talauci) su na kuma fatan ka yi amfani da damarka wajen sama musu saukin rayuwa. A wadata ‘kasa da abinci, a samar da ayyukan yi cikin sauri, gami da rage farashin kayan masarufi. Ba shakka hakan zai taimaka al’umma su samu sukuni.

Ya mai girma Shugaban ‘kasa, ina fatan Allah ya ba ka dama da ikon duba wannan Wasika da kuma yin abin da ya dace kan sakon da ta ‘kunsa.

Na gode!

Daga naka,

-Garba Tela Hadejia
Juma’a, 26/4/2019.

Leave a Reply