BINCIKE NA NUSAMMAN YA NUNA YADDA DANGIN MIJI KO DANGIN MATA SUKE LALATA DA ‘YA’YAN ‘YAN UWANSU -Aunty Ummancy

0
1030

Daga Datti Assalafiy

Shin Iyaye! Ko kunsan Akasarin Kananan Yara ‘Yan Uwansu Na jini ne Ke Soma Lalata Dasu?

Wannan bincike ne na Musamman da yake bukatar Karatun ta Natsu domin daukar matakan da suka dace waken shawo kan wannan Matsalar da take neman zama ruwan Dare a Tsakanin Al-umma.

Al-amarin yanada ban tsoro, akwai takaici a cikinsa Cin Amana shi ne abunda wannan binciken ya gano dangane da yadda ‘yan uwa na jini ne suka fi yawaita bata yara mata da aka aminta dasu aka saki jiki da su.

Daga watan Janairun na Shekarar data gabata zuwa watan Janairu sabuwar shekarar nan ta Dubu Biyu da Sha Tara 2019, Wani Mutum da matarsa sunyi aikin baiwa samari da ‘yan mata Shawarwari wanda yawansu a cikin littafin su na adana bayanan sirri na irin wadannan mutanen suka kai Dubu Goma sha Biyar da Dari Uku da Goma sha Daya. (15,311).

A cikin wannan jimmilar Dubu Takwas da Hamsin mata ne, Dubu Biyar da Dari Bakwai ‘yan mata ne wadanda basu haura shekaru Ashirin da Biyar 25 ba.

A cikinsu Dubu Hudu da Dari Biyu da Hamsin sun taba zina, Sannan Dubu Uku da Dari Shidda ‘yan uwansu na jini ne sune suka Fara yin Lalata dasu.

Wannan yasa muka yanke shawarar fitowa da wannan binciken namu domin kowa ya gani musamman iyaye domin nazari da kuma daukan mataki na kiyaye afkuwar ire iren wannan lamarin.

Babu shakka Addini da Al-ada sun baiwa ‘yan uwa damar kusantar ‘yan uwansu koda kuwa mata da maza ne, Da wannan ne shima Shedan yayi Alkawarin sai yayi amfani da wannan damar domin ganin ya cusa son zuciya a tsakanin muharramai domin cutar dasu.

Akasarin wadannan ‘yan matan basu wuce shekaru 10, zuwa 13 ba a lokacin da akai masu wannan Mummunan Aikin ba ”

Wata daga cikin Yaran da akaba Shawara ta Bayyana yadda ta tsinchi kanta a cikin wannan Mummunan Lamarin tace: Bani mantawa ni dai kanin mahaifiyata ne ya soma lalata dani, tun ban yi wayau ba yake haba-haba dani har lokacin da na soma wayau.

Kamar yadda kika ganni inada girman jiki domin wasu idan na fadamusu shekaruna basa yarda saboda yanayin jikina, Nayi saurin fito da Nonuwa tun kamin na soma Al-ada.

“Akwai wata Rana ne da shi kawuna ya zo Gidanmu a lokacin kuwa babu kowa a Gidan sai ni kadai, Kuma daman can ya sha yi mani wasannin banza yana taba mani nonuwa tun ma bai kai haka ba, A wannan ranar ne dai ya samu yayi Lalata dani, A gaskiya ba wai ya tilastani bane, domin tunda na soma wayau na gane yana sha’awata duk da nasan kanin mahaifiyata ne, yakan mani wasannin da ni kaina inaso idan muka faki idanuwan mutane.

Kuma daga wannan ranar na soma sanin Da namiji a dalilinsa”.

Binciken namu ya nuna cewa cikin wadannan ‘yan matan da ‘yan uwansu na jini suka soma lalata dasu, kannen iyayensu mata sunfi yawa.

Domin kashi 70 cikinsu kawunansu ne suka Fara Kauda/keta budurcinsu, Wanda masu karatu zasu fi tunanin ‘yan uwansu na ‘Dan wa da Dan kani ne zasu fi aikata hakan, amma ina wannan sune ma suka zo kashi na uku baya ga mazan iyayensu mata.

Sai ‘ya’yan yayye ko kanne a na uku da kannen mahaifa sai kadan daga wadanda iyayensu da suka haifesu ne suka soma yin Lalata dasu.

Wannan yasa muka sake dubawa domin sanin ko mi yasa su kanne iyaye mata suka fi yawa cikin mutane masu lalata da jininsu.

Sai muka fahimci cewa irin yarda da Amana da uwa take yiwa Dan uwanta yasa maza masu wannan halin cin wannan Amanar.

A duk lokacin da aka ce ga ‘yarku ta fita da Dan kanin Mijinta ko Dan yarta ko kanwata, ana kaiwa wani lokaci hankalin iyayen bazai samu natsuwa ba, cikin abunda zai shigo ransu kuwa harda tunanin Lalata a tsakaninsu.

Haka nan da za ace kun fita kun barsu a Gida su Biyu nan ma babu kwanciyar hankali kuna tunanin komai na iya faruwa.

Amma idan da kanin matarka ne ko kaninka babu wani abunda zai zo maka na tunanin wani Al-‘amari irin wannan ko da kuwa dukkaninsu kusan shekarunsu guda sabanin Dan wanka ko kaninka ko na matarka. To fa anan gizo yake tsakar.

Da wannan aminta ne da kuma haramcin dake tsakaninsu yasa ake kauda kai.

” Wata Yarinya itama ta bayyana yadda kanin mamanta har ciki yayi mata, tachi gaba da cewa, Domin tun ina karama yake dorani akan cinyansa har na soma girma sai ya rika goga mini Azzakarinsa a gabana kuma ya tsoratani da cewa kada na fadawa kowa.

Yana matukar nuna mini kauna, kuma iyayena sunyi matukar yarda da shi, Shike kaini makaranta shike daukoni.

Da zani ummura da Aikin Hajji dashi aka hadamu, A lokacin da na nace inason zuwa Dubai naga Garin saboda yadda dashi aka hadamu aka bamu kudin hotel na kwanaki 10 kowa da dakinsa amma a daki guda muke kwana.

” Kuma bazaka taba ganin wasu alamun cewa akwai wata alaka ko soyayya a tsakaninmu ba.

Domin ana ganin shine mutumin da nake shakka da tsoro iyayena kuma basusan shine mutumin daya lalatani ba, Ya zama bana iya barci idan ba a jikinsa ba, gaskiya abunda yasa ma nazo wajenki #Aunty_Ummancy inaso ne ki bani shawarar yadda zan daina sonshi ina son yin Aure tunda nasan bazan Aureshi ba”.

Masu Auren maza sunada yara mata suma suna cikin wannan masifar, domin binciken ya tabbatar da cewa mazajen wasu matan sun taimaka matuka wajen lalata musu yara duk kuwa da haramcin Auratayya dake tsakaninsu.

Ga Bayanin wata Yarinya tace “Ina da shekaru 10 a duniya mahaifiyata ta Auri mijinta bayan mahaifina ya rasu, Tun bamu shekara a Gidansa ba ya soma nuna alamun yana son yin Lalataa dani.

Da yake shi ba wani mai tsauri bane, yana da son mutane kuma yana daukata tamkar ‘yar cikinsa duk da yanada wasu yaran matan amma basu kaini shekaru ba.

Yana daukanmu muje ya mana sayayya amma nawa daban yake mani,Tun ban fahimceshi ba har dai na soma fahimtarsa.

Akwai wata rana mahaifita ta fita unguwa nayi wanka ina shafa mai kawai sai naji ana wasa da nonuwana ta bayana kamin dai nace wani abu aikin gama ya gama, kuma daga wannan ranar lokaci zuwa lokaci muna yi.

sai dai da kansa yace mu daina kuma gaskiya ya daina amma ni kuma na saba inada samari da nake samunsu idan ina sha’awa, sai dai kamar yadda na fadamiki yanzu na samu wanda zan Aura shine na miki bayanin matsalar da yanzu ake ciki”, Wannan ma mijin mamanta ne ya soma lalata da ita.

Hirarraki suna da yawan gaske, Sai dai abin bukata shine iyaye su fahimci irin hadarin da suke ciki domin sanya idanuwa a inda zasu iya saka idanuwan.

Sai dai kuma irin wasu da iyayensu da suka haifesu da yayyensu ne suka soma lalata dasu su kuma yaya za ayi? Da akwai ‘yan mata uku cikin wadanda muka baiwa shawara biyu cikinsu iyayensu da suka haifesu sune suka lalatasu, guda kuwa wanta ne uwa daya uba daya.

Bayaga mata, cikin maza suma mun samu wadanda kannen iyayensu ne suka soma koya musu Lalata, wasu kuwa ‘yan uwan iyayensu ne suka yi luwadi dasu wal Iyazu Billah.

Manufar fito da wannan binciken shine mu na bada shawara ga Al-umma su fahimci babu abunda zuciya bazata iya aikatawa ba idan Mutum ya baiwa shadan damar yin hakan.

Yanada da kyau iyaye suyi iya abunda zasu iya yi domin sauke hakkin dake kansu na baiwa ‘ya’yansu da yaran dake karkashin kulawarsu.

Kada iyaye su dauka wane bazai iya yin haka ba, haka kuma kada iyaye suyiwa na kusa dasu mummunar zato ko fahimta, illa dai wannan binciken yana son ya ankarar da iyaye ne su fahimci yanzu haka akwai abubuwa marasa kyau dake gudana a cikin gidajensu ko dai basu maida hankali wajen ganowa ba, ko kuma an tsorata wadannan yaran da ake cutarwa akan kada suyi magana.

Allah Ya shirya, Ya kuma tsaremu da iyalanmu Ya bamu ikon sauke nauyin tarbiyan dake kanmu Ya kuma sa mufi karfin sha’awan mu Amin.

Dan Allah duk Wanda yaga sakon nan da kuma karanta shi har karshe ya fahimta yayi kokarin Kaishi gaba domin wasu su ankare su Amfana Allah ya zaunar damu lafiya Amin.

Leave a Reply