GWAMNA DR. ABDULLAHI UMAR GANDUJE ZAI BA WA KANAWA MAMAKI:-

0
329

Daga Bashir Abdullahi El-Bash

Ba sai an fada ba, sanin kowa ne, cikin wa’adin zangon mulki na farko kawai al’ummar Jihar Kano sun jima ba su yi gwamnan da ya wanzar da ayyukan raya ‘kasa a birni da karkara irin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ba.

Haka zalika, Kanawa sun ji ma ba su yi gwamnan da a wa’adin zangon mulkinsa na farko ya tattaba fannonin rayuwar al’umma daban-daban ba.

Misalin, idan mu ka yi duba da fannin Lafiya za mu fahimci mai girma gwamna ya samar da kayan aiki da inganta Asibitocin gwamnati a Jihar Kano.

Fannin ruwan sha da tituna kuwa, anan ma mai girma gwamna ya yi kokari matuka wajen samar da ruwan sha da tituna gami da gadoji ta sama da ta ‘kasa duk domin samar da walwala ga al’ummar Jihar Kano da kuma rage cinkoson ababen hawa hadi da bunkasa tattalin arziki.

Fannin Ilimi ma mai girma gwamna bai bar shi haka nan kara zube ba, domin kuwa ya samar da ‘karin inganci kan harkar Ilimi a Jihar Kano, ‘dalibai da dama da ke karatu a ‘kasashen waje ya biya musu kudin makaranta. Gami da biyan kudin jarrabawa ga ‘daliban cikin gida wadanda su ka cika ‘ka’ida.

Haka nan fannin Noma domin a baya har matemakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbanjo ya gayyato ya zo ya kaddamar da kayan tallafin da aka rabawa manoma, wato kayan aikin Noma irin su Tantan.

Hatta ‘yan Mata masu sana’o’i ba a bar su a baya ba, domin kuwa har tallafin jari da kayan gudanar da sana’a mai girma Gwamna ya raba musu a kwanakin baya. Inda mata masu toya a wara su ka rabauta da tallafin risho da sauran kayan da za su tallafa musu wajen cigaban sana’o’insu.

Haka zalika su ma maza Matasa masu sana’o’i daban-daban mai girma gwamna ya ba su jari da tallafin bunkasa sana’o’insu da kasuwancinsu daban-daban a baya.

Ba shakka, sannu a hankali mai girma gwamna zai cigaba da ba wa Kanawa mamaki a wannan zangon mulki na biyu ya hanyar cigaba da zazzaga musu ayyukan raya Jiha a birni da karkara.

Leave a Reply