ME KA SANI GAME DA GIDAUNIYAR GANDUJE ?

0
232

Daga Bashir Abdullahi El-Bash

Hakika, akwai bukatar al’ummar ciki da wajen Jihar Kano su san wani abu game da Gidauniyar Gwamnan Jihar Kano, Dakta, Abdullahi Umar Ganduje duba da irin kyawawan manufofin da ke kunshe cikinta.

(Ganduje Foundation), ko kuma gidauniyar Ganduje, wata gidauniya ce da mai girma gwamnan Jihar Kano ‘karkashin tutar jam’iyyar (APC) Dakta, Abdullahi Umar Ganduje ya assasa a Jihar Kano.

Me Ake Nufi Da Gidauniya: idan an ce gidauniya, ana nufin wani tsari na musamman ko wasu kudade da wani mutum ko wasu mutane ko wata ‘kungiya za ta ware ko ta tara domin gudanar da wasu ayyuka na musamman da za su shafi rayuwar ‘dan adam.

Wadanne Irin Ayyuka Gidauniyar Ganduje Ta Ke Yi: mai girma gwamna, ya kafa wannan gidauniya ne domin gudanar da ayyuka na musamman kamar:

Tallafawa Malamai da inganta harkokin Ilimi, da bunkasa addinin Musulunci ta hanyar gina masallatai da kuma jawo ra’ayin wadanda ba musulmai ba su karbi Musulunci.

Haka kuma, ya na daga cikin ayyukan wannan gidauniya ta mai girma gwamna Ganduje tallafawa marasa lafiyar da jinyoyinsu su ka fi ‘karfin aljihunsu ta hanyar ‘daukwar dawainiyarsu da jibintar al’amuransu.

A Ina Gidauniyar Gwamna Ganduje Ta Ke Samun Kudaden Gudanarwa: ba shakka mai girma gwamna Ganduje da kansa ya ke tafiyar da wannan gidauniya. Babu wata gidauniya ko wasu masu hannu da shuni da su ke ba shi gudunmawa kamar yadda sauran gidauniyoyi su ke samu.

Daga dan abin da ya ke samu cikin albashinsa ya ke ware kudade na musamman domin gudanar da ayyukan wannan gidauniya.

Wadanne Nasarori Gidauniyar Ganduje Ta Cimma: ba shakka, wannan rubutu ya yi kadan ya hadidiye duk wasu ayyuka ko nasarori da wannan gidauniya ta samu zuwa yau.

Sai dai a takaice, Gidauniyar Ganduje ta samu nasarar Musuluntar da dumbin Maguzawa a ciki da wajen Jihar Kano.

Ta kuma samu nasarar kula da gyaran idon dumbin mutane masu fama da lalurar ido. Gami da tallafawa marasa lafiya da dama.

Gidauniyar Ganduje ba ta tsaya anan ba, domin ta samu nasarar gina Masallatai da dama, kuma daga cikin wuraren da ta gina masallatan har da jami’ar kimiyya da fasaha ta garin Wudil.

Kamar yadda na fada a baya, nasarorin su na da yawa, kuma ana kan cigaba da cimma wasu.

Ba shakka, idan mu ka yi duba da gwamnonin Arewa da ma Nageriya gaba daya, a iya cewa babu wani gwamna da ya ke da gidauniya ta musamman da ya ke gudanar da ayyukan jinkai da bunkasa addinin Allah sai mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta, Abdullahi Umar Ganduje (Khadimul Islam).

Allah ya kara masa karfin gwiwar cigaba da wadannan ayyukan alkhairai.

Leave a Reply