RAHOTON ‘YAN KUNGIYAR SHI’AH (IMN) SUNCE AKWAI HARSASHIN BINDIGA A JIKIN MATAR ZAKZAKY

1
1636

Daga Datti Assalafiy

Ga rahoton da ‘yan shi’a suka fitar kamar haka:
“Likitoci daga Kasar waje sun fara duba Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa Malama Zeenah a a ranar Alhamis 25/4/2019, wannan hoton Shaikh din ne tare da Likitocin.

Shaikh Ibraheem Zakzaky na tsare tun fiye da Shekaru 3 da suka gabata, duk kuwa da yau fiye da Shekaru biyu da kotun Nijeriya a Abuja tace a sake shi a biya shi diyyar tsarewar da aka masa ba bisa ka’ida ba.

A ranar 22 ga Junairun 2019 ne babban lauyan Shaikh Ibraheem Zakzaky, Mr Femi Falana SAN, ya mika bukata ga kotu a kan ta bari a bar Shaikh Ibraheem Zakzaky ya je ya nemi magani a wajen kwararrun Likitoci a waje.

Sai kotun ta ba da umurni a zo da Likitocin daga ko ina su duba Shaikh din su ga yanayin jikinsa sai su ba kotu rahoto, sannan ta duba yiwuwar bari a fita da shi ko ai masa magani a nan.

Shaikh Zakzaky na fama da rashin lafiya sosai, sakamakon harbin da sojoji suka masa a kafa da hannu da ido, har ya zama ya rasa idonsa guda daya.

Haka ma Matarsa Malama Zeenah Ibraheem, ta na fama da raunin harsasai a yayin da har yanzu akwai wadanda ba a cire su a jikinta ba, har ma ba ta cika iya tafiya da kafarta ba….” ~Rahoton ‘yan shi’ah.

Abinda ya ja hankali na a cikin wannan labari da ‘yan shi’ah suka wallafa shine wai har yanzu akwai harsashin bindiga a jikin matar Zakzaky Madam Zeenatu, ‘yan shi’ah suna nufin babu likitocin da zasu iya cire mata harsashin ne aka bari a jikinta ko me suke nufi?

Bindigar da sojojin Nigeria suke rikewa AK47 ne, kuma hoton da muka gani tare da sojoji lokacin da suka kama Zakzaky kafin su sukashi a wilbaro bindiga kirar AK47 ne a tare dasu, idan ya tabbata sojoji sun harbi Zakzaky da matarshi to da bindiga kirar AK47 ne.

Abinda muka sani game da bindiga AK47 ya wuci ‘yan shi’ah su fitar da irin wannan rahoto don su wautar da hankalinmu, ban taba ganin wanda aka harbeshi da bindiga kirar AK47 a harbin kusa (close range) ace wai harsashin bai ratsa jikin wanda aka harba ya fita ba, karfin da harsashin AK47 yake dashi ya wuce wannan.

Harsashin AK47 dalma ne, da zaran an harbashi wuta yake zama ya narke yabi iska, ya kanyi gudun mita dari hudu, misali tsayin filin kwallo sau hudu, ana iya samun harsashin AK47 a jikin mutumin da aka harbeshi daga nesa (long range), kuma harsashin guba ne, babu yadda za’a ce harsashi ya shekara 3 a jikin mutum ya zauna lafiya kamar yadda muke ganin Zakzaky da matarshi garau a wannan hoton.

‘Ya shi’a sunce kwararrun sojoji ne suka budewa Zakzaky wuta har sai da harsashin bindigoginsu ya kare lokacin da suka tsaya a kanshi zasu kama, ko ina jikinsa bullet ne, akwai wadanda sukace sai da Zakzaky ya mutu bayan kwana uku Allah Ya dawo masa da ranshi saboda tsabar karya, AK47 ba bindigar wasan yara bane, da fatan magoya bayan Zakzaky zasu dena wautar da hankalin ‘yan Nigeria.

Allah Ka bawa Zakzaky mafita na alheri, Ka shiryar dashi tafarkin musulunci.

1 COMMENT

Leave a Reply