Rashin albashi na tsawon shekaru 7 ya jefa malamai cikin kuncin rayuwa – A jihar Ekiti

0
126

Daga Anas Saminu Ja’en

Malaman sakandare a jihar Ekiti wadanda tsohon gwamnan jihar Ayodele Fayose ya dauka aiki tun shekarar 2018 sun gubatar zanga-zanga a jiya, domin rashin biyan su albashin tsawon wata 7, kuma sun roki gwamna Kayode Fayemi da ya tausaya masu ya biya su wannan albashin da suke bi bashi domin ya share masu kukansu.

Kuma Malaman sunce fitowarsu zanga-zangar ta kasance domin janyo hankalin gwamnati zuwa gare su, sai dai kamar yunkurin nasu baiyi wani alfanu ba saboda har yanzu ba ace dasu komi ba, kamar yadda daya daga cikin masu zanga-zangar, Bayo Omoyemi, ya shaidama ‘yan jarida cewar a madadin abokan aikinsa sun rubuta wasika zuwa ga gwamna Fayemi da matarsa tare da mataimakin gwamnan da kuma masu sarautun gargajiya, inda suke rokon su da su ceci rayuwarsu “a fiddasu daga halin ni ‘ya sun da suke ciki.

Ya kara da cewar muna son gwamnati ta kula mu domin magance mana damuwar mu, kasancewar yanzu ana hutu, kafin a koma hutun zango na uku yakamata ayi wani abu kan wannan matsala, domin da dama daga cikin mu basu iya biyan kudin haya a wuraren da suke zaune da wasu matsaloli daban-daban dai na rayuwa muke fuskanta sakamakon rashin albashin inda muke rokon gwamnati na ta dubi wannan lamarin da idon rahama ayi wani abu a kai.

Leave a Reply