TSAKANIN AUREN AURI-SAKI DA LALATA ‘YA’YAN MUTANE

0
584

Daga Datti Assalafiy

Ance Adam A Zango ya auri matarsa ta shida, wato mutum ne mai dabi’ar auri saki, wannan ya jawo masa suka da zagi, akwai wanda na gani yana cewa ya dace iyaye su hana bada auren ‘ya’yansu wa Adam A Zango.

Auren auri saki ba abune mai kyau ba, malamai sune halal din da Allah baya so shine mutuwar aure, Malamai sunce idan anyi sakin aure Al’arshin Allah sai ya gurgiza, sannan shi kuma iblis babban abinda yafi so kenan mutuwar aure, don haka ba abune mai kyau ba.

Sai dai abin takaici, wannan matsala na yawan auri saki har manyan Malaman da duniyar musulunci take jin muryansu dabi’ar da suka koma kenan yanzu auren auri saki, wanda a tsammani ya kamata ace jahili ne zai rungumi wannan mummunan dabi’ah na auri saki.

To amma tsakanin auren auri saki da lalata da ‘ya’yan mutane wanne yafi sassauci? babu shakka auri saki yafi sassauci, idan ma da akwai zunubi to ko kusa bai kama kafar lalata da ‘ya’yan mutane ba.

Indai Adam A Zango baya lalata da ‘ya’yan mutane to hakan yafi masa alheri, bai kamata ana zaginsa da ci masa mutunci ba tunda manyan Malamai ma sunayi illa iyaka a samu wasu malamai da yake ganin darajarsu su masa nasiha don ya fahimci cewa idan aka yiwa ‘ya’yansa mata auren auri saki shima ba zaiji dadi ba.

Allah Ya tsare nana imanin mu Amin.

Leave a Reply