HANYOYI GUDA BIYU DA ZA’A KUBUTAR DA ZAINAB DAGA HALAKA – DATTI ASSALAFIY

0
1510

Daga Garba Tela Hadejia

Maigirma Sanata Shehu Sani ya fitar da sanarwa a shafinsa na Twitter yake kira ga iyayen Zainab wacce aka saka muggan kwayoyi a jakarta aka kamata a Saudiyyah aka tsare.

Sanata Sani yace inda iyayen Zainab zasu rubuta takardan koke cikin gaggawa su aikawa majalisar Dattawan Nigeria su fadi bayanin tuhumar da ake yiwa ‘yar su a Saudiyyah cewa bata da laifi, Sanatocin Nigeria zasu tattauna sannan su dauki matakin gaggawa da zai kai ga kubutar da Zainab.

Bayan haka yanzu wani yake sanar dani cewa; wannan baiwar Allah da aka sa wa kwaya acikin jakarta, gaskiya mafita guda dayace anan, tunda an tabbatar dacewa wannan ba halinta bane, to mai zai hana aje asami tsohon gwamnan jihar Sokoto wato Attahiru Bafarawa?

Domin shi Attahiru Bafarawa yana daya daga cikin masu alfarma da daraja mai girma a gurin mahukuntan Saudiyyah ga wanda bangaren binciken laifin hakan ta faru dasu a Kasar ta saudiyya, zaiyi magana da wadanda hakkin abin ya shafa, sun bashi wannan alfarma saboda yaddar da suka masa.

Yanzu dai ga dama ta samu guda biyu, ya rage wa iyayen Zainab suyi abinda ya dace cikin gaggawa kafin a fille kan ‘yar su, Kuma muna fata mahukuntan Saudiyyah zasu dena yin gaggawa wajen fille kawunan mutane.

Allah Ya sauwake Ya kubutar da Zainab Amin.

Leave a Reply