SHUGABA MUHAMMADU BUHARI YA BA DA UMARNIN CETO RAYUWAR ZAINAB:-

0
3341

Daga Datti Assalafiy

Kamar yadda rahotanni su ka tabbatar, Zainab Habib Aliyu, ‘daliba ce ‘yar asalin Jihar Kano da ta gamu da iftila’i inda jami’an tsaron ‘kasar Saudiyya su ka kamata da zargin safarar miyagun ‘kwayoyi ya yin da ta je aikin Umrah!

Kuma rahotanni sun shaida dacewar wasu gurbatattun mutane ne a filin saukwa da tashin jiragen sama su ke sakawa duk wanda tsautsayi ya fada masa ‘kwayoyi cikin jakarsa, kamar yadda su ka yi wa Zainab.

Sai dai, tuni mai girma Shugaban ‘kasar Nageriya, Malam Muhammadu Buhari ya ba wa babban lauyan gwamnatin tarayya umarnin yin duk mai iyuwa domin ganin an samu nasarar ceto rayuwar Zainab daga kisa.

Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin babban mai taimakawa Shugaba Muhammadu Buhari kan harkokin ‘kasashen waje.

-Garba Tela Hadejia
Litinin, 29/4/2019.

Leave a Reply