TSOHON SHUGABAN KASA JONATHAN YA ZALUNCI AREWA TA KARKASHIN KASA – DATTI ASSALAFIY

0
1236

Daga Datti Assalafiy

Wannan hotuna da ake gani, gini ne na wata Jami’ah mai suna Nigeria College of Petroleum Studies Kaduna (NCPSK), makarantar tana nan a Rigachukum kusa da Kasuwar Duniya.

An fara gina makarantar a lokacin shugaban Kasa marigayi Umaru Musa ‘Yar adua, majalisar zartawa (federal executive council) a lokacin sun amince za’ kashe kudi biliyan sha hudu da miliyan dari biyar (N14.5b) daga petroleum development fund (PTDF) domin gina wannan jami’ah.

An fara aiki tukuru domin gina jami’ar, amma bayan rasuwar shugaban Kasa Umaru Musa ‘Yar adua, sai Jonathan ya hau, yana zuwa sai aka dakatar da aikin, amma akwai takwarar ita wannan makaranta a jihar Delta da aka gina, wadda ina kyautata zaton an ma bude ta tun shekarar da ta gabata.

Kuma dama can akwai wata makaranta Petroleum Training Institutes a jihar Delta din wadda take tun shekarar 1973, gashi yanzu sun kara samun jami’a sukutun wadda a yankin arewa bamu da ita.

A shekarar 2016 ‘yar majalisar tarayya Hajiya Aisha Jibril Dukku wacce ke wakiltar Dukku da Nafada a jihar Gombe, ta kai kudiri gaban majalisa don a dawo da batun gina wannan jami’ah a Kaduna, amma har yanzu babu masu mara mata baya.

Shugabannin Arewa tun daga kan shugaban kasa Buhari, yanzu ne kuke da damar da zaku samar da wannan jami’ah a arewa domin arewa da ‘yan arewa su amfana.

A kullun tsohon shugaban Kasa Jonathan ya bayyana a garemu a matsayin babban makiyin arewa, duk wani abinda zai kawo cigaba a arewa wanda marigayi Umaru Musa ‘Yar Adua ya assasa, bayan rasuwarshi Jonathan ya dakatar, Jonathan bai assasa komai a arewa ba sai cin amana da ta’addanci.

Allah Ka juyo da hankalin shugaba Buhari zuwa kan wannan jami’ah, Ka bashi ikon tabbatar da ita Amin

Leave a Reply