YA ZAMA DOLE A CETO RAYUWAR ZAINAB HABIB ALIYU – DATTI ASSALAFIY

0
1005

Daga Datti Assalafiy

Zainab Habib Aliyu tana bukatar taimakon al’umma da shugabanninmu musamman na nan Arewa, haifaffiyar kano ce Daliba a Jami’ar Maitama Sule dake nan Kano.

Ta hadu da iftila’i a hanyar shiga Saudi Arabia don aikin umrah, tana tare da Mahaifiyarta da ‘yar uwarta, aka samu wasu mutane marassa tsoron Allah suka saka muggan kwayoyi a jaka aka saka lambar tag da akayi mata awo, sakamakon haka aka kamata a Saudiyyah aka kaita kurkuku, wanda karshe hukuncin kisa ne za’ayi mata.

Bincike ya nuna wannan yarinya bata da laifi, babu wani abu da ya hada ta da miyagun kwayoyi, wajen bincike an kama wasu mutane ma’aikatan filin jirgin sama na Malam Aminu Kano wanda binciken ya tabbatar suna da hannu wajen cutar da wannan yarinya.

Ina gwamnatin tarayya? hakki ne a kanku ku sa baki a ceto Zainab daga halaka.
Ina Gwamnatin Kano? kina da hakki wajen saka baki a ceto Zainab.
Ina Sarkin Kano? kana da jarumta wajen bin hakkin wanda aka zalunta, nasan zaka iya zuwa har kasar Saudiyya don kubutar da Zainab.
Ina Sanatocin mu na Kano? kuna da gudunmawa da zaku bayar wajen saka baki a matakin kasa don kubutar da Zainab.

Yadda aka tabbatar Zainab bata da laifi wallahi idan ta rasa ranta ta wannan hanya dukkan wadannan mutane kuna da laifi, kuma sai Allah Ya tambaye ku akan sakaci da rayuwar wannan yarinya. -Ismail Lamido

Ya Allah Ka kubutar da Zainab da dukkan wanda suka fada wannan hali na banji ba ban gani ba.

Leave a Reply