GARKUWA DA MUTANE (KIDNAPPING) BAKON ABU NE A NIGERIA – DATTI ASSALAFIY

0
710

Daga Datti Assalafiy

Mun samu labari jiya masu garkuwa da mutane sun tare hanyar Kaduna zuwa Abuja suka budewa motoci wuta, kuma ance wai sun kama mutane da dama sun tafi dasu jeji.

Wannan abin ya faru a daidai lokacin da gwamnatin Baba Buhari take kokari wajen daukar kwakkwaran matakin da ya dace akan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

A jiya ne naga Sanata Shehu Sani ya wallafa rubutu a shafinsa na Twitter yake bada shawaran cewa hanyar Kaduna zuwa Abuja tana bukatar a samar da jiragen leken asiri, da kuma jirage masu saukar ungulu da zasu dinga shawagi akan hanyar, sannan a kula da daukar nauyin jami’an tsaro da zasu tunkari masu garkuwa da mutane a yankin.

Wannan shawara da Sanata Shehu Sani ya bayar abune mai kyau, sai dai duk da wannan idan babu kwararrun jami’an tsaro da suke da horo na musamman akan yaki da masu garkuwa da mutane to da wahala a kai ga gaci.

Matsalar garkuwa da mutane abune bako a cikin sha’anin tsaron Nigeria, kuma gaskiya bamu da kwararrun jami’an tsaro sosai a bangaren yaki da garkuwa da mutane idan aka dauke kwararru irinsu DCP Abba Kyari, DSP Ahmed Mustapha da makamantansu wanda yake kalilan ne da suka taba zuwa Kasar Isra’ila aka basu horo na musamman akan yaki da kidnappers.

A Kasar Isra’ila da Amurka ne suke bada horo na musamman akan yaki da garkuwa da mutane, su tuntuni sunyi tanadi akan wannan matsalar, Nigeria tana bukatar ta dauki nauyin adadi mai yawa na jami’an tsaro ta tura su Kasar Isra’ila su samu horo.

Yaki da garkuwa da mutane a cikin kashi 100 kashi 25 ne kacal idan ta kama sai ayi amfani da karfin bindiga, amma kashi 75 cikin 100 ilmi ne da dabaru ake bukata, wanda dole sai an damu lokaci an karantar da jami’an tsaro a kansa kuma an wadatashi da kayan aikin da suka dace.

Inda ace wannan bayanin zai riski Sanata Shehu Sani to ya duba da idon basira, ya gabatar da kuduri gaban majalisar su, gwamnatin Nigeria ta dauki nauyi a tura jami’an tsaro suje gurin yahudawan Isra’ila ko Amurka su koyo ilmin yaki da masu garkuwa da mutane.

Yanzu a Nigeria duk inda akayi batun yaki da masu garkuwa da mutane sai kaji ance ina DCP Abba Kyari? DCP Abba Kyari aiki ya masa yawa jama’a, wallahi sadaukarwa yake, shima ‘dan adam ne kamar kowa, yanzu haka baya Nigeria, yana karban wani horo na musamman da hukumar ‘yan sandan kasar Amurka masu binciken manyan lafuka da ta’addanci Federal Bureau of Investigation (FBI)

Yadda shekarun baya aka tura DCP Abba Kyari Kasar Isra’ila yaje ya karbi horo kuma ake cin amfanin horon da ya samu, ya kamata yanzu ma gwamnatin Nigeria ta tura jami’an tsaro masu yawa suje su karbi irin wannan horon su dawo su tunkari matsalar garkuwa da mutane da kullun yake karuwa kamar wutar daji musamman a arewan Nigeria.

Duk wanda bayanin nan ya bata masa rai yayi hakuri, amma wannan shine gaskiyar al’amari indai ana so a kawo karshen masu garkuwa da mutane a Nigeria.

Allah muke roko Ya kawo mana karshen masifar garkuwa da mutane a Nigeria Amin

Leave a Reply