MAKIYAN SAUDIYYAH SUNJI KUNYA – DATTI ASSALAFIY

0
399

Daga Datti Assalafiy

Alhamdulillah ga nan Zainab tare da ma’aikatan ofishin jakadancin Nigeria dake birnin Jiddah a Kasar Saudiyya bayan an sakota, alherin Allah Ya kaiwa shugaba Buhari.

Anan dandalin facebook mun tattara dukkan batanci da cin mutuncin da makiya gwamnatin Saudiyyah sukayi.

Akwaisu kamar haka:
-Rubabbun musulmai ‘yan boko aqeedah
-Manyan da kananun ‘yan iska
-‘Yan nanaye har ma da wadanda ake zarginsu da madigo
-Masu bakar aqeedah na kyamar ahlussunnah, Yau Allah Ya kunyata wadannan mutanen banza, bisa cin mutunci da batancin da suka yiwa Saudiyyah akan batun Zainab.

Ita dai Zainab wannan shine jarrabawan da Allah Ya mata a matsayinta na musulma, kuma Allah Ya na jarraba bayinshi da Ya fi so ne, duk musulmin da yake rayuwa ba tare da yana fuskantar jarrabawa ba a rayuwa malamai sunce ya binciki imaninsa, Allah Zai iya jarraba musulmi da komai.

Abinda ake fata duk runtsi duk wuya musulmi yayi kokarin tabbata a kan gaskiya, duk wanda ya taki gaskiya koda jarrabawa tazo an masa sharri to Allah Zai kubutar dashi, gaskiya zatayi halinta.

Allah Ya sa abinda yaru da Zainab ya zama darasi garemu gaba daya.

Leave a Reply