MUMMUNAR ‘KADDARA DA KYKKYAWAN SAKAMAKO:-

0
1057

Daga Garba Tela Hadejia

Kafin na yi nisa cikin bayani kan abin da ya kamata jama’a su sani game da kykkyawan sakamakon da ya biyo bayan mummunar ‘kaddarar da ta fadawa wannan baiwar Allah Zainab Habib Aliyu.

Wacce jami’an ‘kasar Saudiyya su ka kama da zargin safarar miyagun ‘kwayoyi.

Zan fara da godewa Allah da ya ‘kaddara mata samun ‘yancin rayuwa daga tarkon mutuwa da ya jarrabata akai.

Zan kuma yabawa Shugaba Muhammadu Buhari duba da yadda ya ba da umarnin yin duk mai iyuwa wajen ganin hukumomi a ‘kasar Saudi sun fahimci gaskiyar al’amari sun sake ta.

Ko shakka babu, kamu da tsarewar da aka yi wa Zainab, ‘kaddara ce mummuna ta fada mata. Amma kuma a iya cewa wannan mummunar ‘kaddara ta haifar mata alkhairai masu tarin yawa.

Misali:

1. ‘Kila ko a cikin unguwarsu ba kowa ba ne ya santa, amma a sanadiyyar wannan mummunar ‘kaddara ta samu shuhura da daukaka a Duniya gaba ‘daya ta yadda kafafen yada labarai da kafofin sadarwa na zamani (Social Media) su ka yi ta tattaunawa akanta har Allah ya ba da nasara aka kubutar da ita.

2. Haka zalika, ‘dazu a sashen Hausa na BBC an tattauna da wata ‘yar uwarta, ta kuma shaida cewa tunda aka tsare Zainab a gidan jarum na ‘kasar Saudi, ta shiga makarantar nakaltar Ilimin Al’kur’ani mai girma, kuma ta maida hankali akai har ma ya kasance a duk ‘karshen mako in an kafe sunan ‘daliba mai hazaka sai aga Zainab ce. Ta samu Ilimin addinin da ‘kila da a gida ta ke bai zama lallai ta samu ba.

3. Duk da ya ke kurkukun Saudiya ba irin na Nageriya ba ne wajen takura da ‘kunci, amma dai duk da haka ‘dan zaman da ta yi na watanni ba makawa ta fahimci irin radadin da ke tattare da zaman gidan jarum ta kuma koyi darasu masu tarin yawa gami da sanin muhimmancin ‘yanci a rayuwar ‘dan adam.

4. Bai zama lallai gwamnatin Nageriya su ‘kyaleta haka nan ba, akwai iyuwar su tallafa mata kan karatunta ko wasu al’amuran rayuwa na daban domin rarrashi da tausasar zuciyarta ta manta ko kada waccar mummunar jarrabawa da ta shiga ta dameta.

5. Ba shakka, Zainab ta ga jarrabawa, amma kuma jarrabawar ta zame mata alkhairi ta fannoni daban-daban.

Mu na mata maraba da samun kai, tare kuma da addu’ar Allah ya kiyaye gaba.

-Garba Tela Hadejia
Talata, 30/4/2019.

Leave a Reply