SHUGABAN KUNGIYAR ISIS TSOHON JAMI’IN LEKEN ASIRIN MOSSAD/CIA (ISRA’ILA DA AMURKA) YA SAKE BAYYANA

0
647

Daga Datti Assalafiy

Tsohon jami’in leken asirin Kasar Isra’ila da Amurka Mr Abubakar Baghdadi shugaban ‘yan ta’addan duniya na kungiyar ISIS ya sake bayyana a karo na biyu.

Al-baghdadi ya bayyana cikin wani faifan video ta kafar watsa labarai Al-furqan da Amaq mallakin kungiyar ISIS, tun a shekarar 2014 da Abubakar Al-baghdadi ya bayyana a cikin wani Masallaci a birnin Mosul ya shelanta jihadi don kafa gwamnatin Musulunci da karfin bindiga, to bai sake bayyana ba sai yanzu, shekaru biyar da suka gabata kenan.

Shugaban ‘yan ta’addan ya bayyana cikin bacin rai da takaici sakamakon fatattakar mayakansa da sojojin hadaka sukayi a cikin kasar Syria da Iraqi, wanda Saudiyya ta jagoranta, yafito yana ikirarin zai dau fansa, sai dai abin lura anan shine a ina zai dau fansar? Allah Shi Ya barwa kansa Sani.

Sai dai wani abinda yaja hankalin mu shine yadda shugaban ‘yan ta’addan yace akwai wasu kungiyoyin jihadi daga kasashen Burkina-Faso da Mali sun masa mubayi’ah, wannan ya nuna mana cewa zai karkato da ayyukan ta’addancinsa zuwa nahiyarmu ta afirka kenan?

Abin la’akari anan; shikansa Al-baghdadi yasan bashi da tasiri a can inda aka fattakeshi a yankin gabas ta tsakiya, tunda Donald Trump ya zama shugaban Kasa ISIS karfinta kullun raguwa yake, dama Donald Trump ya zargi Barak Obama da laifin kafa kungiyar ISIS tare da basu makamai sukayi karfi a duniya cikin kankanin lokaci.

Ya kamata shugabannin kungiyar kula da tattalin arzikin yammacin afirka (ECOWAS) da kungiyar tarayyar afirka (AU) suyi nazarin kungiyoyin ta’addanci na kasashen Burkina-Faso da Mali a san yadda za’a yi a dakile su tun kafin ISIS ta wadatasu da kayan ta’addanci su addabi kasashen mu

Yaa Allah Ka mana maganin karnukan farautar Kasashen Amurka da Isra’ila Amin.

Leave a Reply