TALAKAWA NA BUKATAR AGAJI DAGA GARE KA:-

0
138

Daga Garba Tela Hadejia

Shugaba Muhammadu Buhari, burinmu a kullum ka yi nasarar da makiya za su ji kunya.

Fatanmu a kullum mulkinka ya zama sanadiyya da silar shigarka gidan Aljannah!

Muradinmu a kullum talaka ya ji dadin da zai ce madallah! Da mulkin Shugaba Muhammadu Buhari a madadin ya ji tsananin da zai ce “tir”.

Mai girma Shugaban ‘kasa, watan Azumin Ramadan ya na daf! Da kamawa, talakawanka kuma musamman al’ummar yankin Arewa su na fama da ‘kunci da talauci gami da hauhawar kayan masarufi.

Agajinka su ke nema a matsayinka na Shugaba ka yi wani abu ko sa samu saukin halin da su ke ciki.

Ba shakka, idan mu ka ‘ki fada maka gaskiya mun cuce ka, su kuma ‘yan uwanmu talakawa mun ha’incesu.

Baba Buhari, ina fatan Allah ya ‘karfafeka, ya ba ka ikon samawa talakawa saukin rayuwa.

-Garba Tela Hadejia
Litinin, 29/4/2019.

Leave a Reply