ABIN DA YA KAMATA AL’UMMA SU GANE:-

0
342

Daga Garba Tela Hadejia

Idan ka fi ‘karfin cikinka, ka fahimci akwai wadanda cikinsu ya fi ‘karfinsu.

Idan ka fi ‘karfin damuwarka, ka fahimci akwai wadanda damuwarsu ta fi ‘karfinsu.

Idan ka fi ‘karfin matsalarka, ka fahimci akwai wadanda matsalarsu ta fi ‘karfinsu.

Ka zama mai iya yaye damuwar wasu in ka na da halin yin haka.

In ba ka da wannan hali, ka zama mai iya kai kukansu inda za a share musu.

In hakan ma ba ta samu ba, ka zama mai sanya su cikin addu’ar samun sauki da mafita wurin Allah.

Baba Buhari ba za mu gajiya da sanar da kai halin da al’ummarka musamman sashen Arewa su ke ciki ba.

Jama’a na fama da talauci, fatara gami da annobar satar mutane domin neman kudin fansa da kashe-kashen rayuka na babu gaira babu dalili a wasu sassan yankin.

Mu na fatan za ka duba ka kuma dauki matakai na gaggawa domin samawa al’umma saukin rayuwa.

Leave a Reply