An Damke Wadanda Suka Yi Garkuwa Da Surikin Dogarin Buhari

0
1070

Daga Yaseer Kallah

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce ta damke wasu mutane da ake zargi da hannu a cikin sace surikin dogarin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A jiya da dare ne wasu masu satar mutane suka yi awon gaba da Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Umar, a gidansa da ke garin Daura bayan ya idar da sallar Magariba.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Gambo Isah, ya ce an damke wasu daga cikin ‘yan bindigar a lokacin da jami’an suka isa gurin. Ya kara da fadin cewa an harbi dan sanda daya a lokacin da suke musayar wuta da ‘yan ta’addan.

Leave a Reply