INA MAFITAR MATSALAR TSARO A AREWA ?

0
279

Daga Garba Tela Hadejia

Kamar yadda jama’a su ka sani, samar da tsaro shi ne alkawari na farko da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa al’ummar Nageriya.

Kuma a iya cewa duk da yadda ya karbi ‘kasar a baya, da kuma yadda ta ke a yanzu tabbas ya yi kokari matuka wajen dakile hare-haren ‘yan ta’adda musamman mayakan Boko Haram.

Sai dai kuma a iya cewa hannun agogo na neman dawowa baya, duba da yadda ake samun sabbin hare-hare a baya-bayannan da kuma sace mutane domin neman kudin fansa.

Kuma matsalar ta ki ci ta ki cinyewa, duba da wannan mu ke fatan Shugaba Muhammadu Buhari zai yi duba ga sasannin tsaro domin binciken kwakwaf! Kan yadda su ke gudanar da ayyukansu.

Duk inda su ke da matsala ko gazawa ko ma hannu cikin wadannan matsaloli, to ya yi gaggawar kakkabe su tare da zuba sabbin zaratan da za su kare ‘kasar da tsare mutuncin ‘yan Nageriya da kimarsu.

Kila yin hakan zai taimaka wajen samun mafitar kan halin rashin tsaro da ke neman addabar wannan yanki.

Leave a Reply