TA’ADDANCIN HAR YA KAI GA HAKA – DATTI ASSALAFIY?

0
1762

Daga Datti Assalafiy

Mun samu labari masu garkuwa da mutane sunje har gida sun dauke babban basarake Magajin Garin Daura Alhaji Musa Umar sun tafi dashi

Magajin Garin Daura ance yana auren ‘yar yayar shugaban Kasa Muhammadu Buhari Hajiya Rakiya, sannan babban dogarin shugaba Buhari Col. Muhammad Lawal Abubakar yana auren ‘yar Magajin Garin Daura mai suna Fatima

Yin garkuwa da Magajin Garin Daura ya shafi shugaba Buhari ta ko’ina, kuma wannan yana nuni ne ga babban barazana na tsaro da ake fuskanta a Nigeria game da yin garkuwa da mutane, wannan abin kunya ne, kuma abin takaici, kamar babu shugabanci a Nigeria!

Sannu a hankali garkuwa da mutane yana kara yawaita, watakila idan akaci gaba da kama manyan mutane mahukunta zasu dauki matakin da ya dace, amma babu shakka ana cikin wani mummunan yanayi.

Talakawa suna dandana kudarsu a hannun masu garkuwa da mutane, an talauta mutane dubbani, International security standard ya amince cewa garkuwa da mutane yana haddasa mummunan karayar tattalin arzikin kasa gaba daya, duk ranar da Allah Ya dawo min da shafina na Datti Assalafiy zan muku cikakken bayani

Allah Ya kawo mana karshen wannan masifa na garkuwa da mutane Amin

Leave a Reply