Matsalar Rashin Tsaro Na Neman Ƙarasa Durkusar Da Arewa

0
250

Daga Anas Saminu Ja’en

Ya kamata dai shugaban nin Arewa manyan jami’an tsaron mu sarakunan gargajiya su ringa kallon irin wannan Bidiyon matar nan dake yawo a shafukan sada zumunta domin ya yi matukar tayarmin hankali tare da kukan zuciya, inda a ciki za kuga inda wata Mata ke kuka da neman addu’ar ‘yan uwa Musulmi sakamakon sace mata ya’yanta da aka yi lokacin da take ƙokarin ceto ɗaliban wata makaranta dake Zamfara.

A cikin wannan bala’in da ya tunkari arewa shi ne kowa yasan bata bar shugaban nin mu ba da kuma mu talakawa, saboda su ‘yan ta’addar haka aka saka su yiwa al’umma ta yadda za su cimma burin su dana iyayen gidan su. Kuma karfa a manta ba bu jimawa da haka aka fara Boko Haram a yakin arewa maso gabashin kasar nan wanda aka yi asarar rayukan miliyoyin mutane aka raba miliyoyi da gidajan su har abun ya tsallako jihar Kano wanda da taimakon Allah da taimakon addu’o’in bayin Allah abun bai yi tasiri ba a Kano, dan haka ya zama wajibi shugaban nin mu su tashi tsaye su hada kansu tare da ajiye bambancin ra’ayi ko akida haka muma talakawa a tunkari wannan masifar ta masu garkuwa da mutane, kowa yasan matsalar nan ta faro ne daga jihohin Kudancin Najeriya har abun ya tsallako arewa irin su jihar Zamfara, Kaduna da sauran su idan har ba a dakile wannan masifar da take neman karasa yankin arewacin Najeriya ba to sai ta mamaye ko ina a arewa.

Haka mu kammu talakawa da muke bari wasu azzalumai ke amfani damu domin aikata wannan aikin na satar mutane to mu ji tsoron Allah talauci ba hauka bane, kuma jama’a idan ana maganar musifa irin wannan ba abune na yin murna ko mayar da shi siyasa ba magana ce ta neman hadin kan kowa domin kawo mafita saboda ba bu wanda ya tsira a cikin wannan ifila’in da yaki ci yaki cinyewa arewa dai tamu ce kuma ba mu da inda yafi arewa akaf fadin duniya duk wanda yake tunkaho da kafafa da arewa wannan shi ne lokacin da arewa ke bukatar a yi wani abu akai musamman masana harkokin tsaro da ‘yan jaridu suma su ringa fitowa domin fadar tsagwaron gaskiyar abun dake faruwa.

Kuma kullum ina kara tunatar da mu cewar matukar galibin mu jama’a ba mu gyara halin mu ba, mun tsarkake zukatanmu tsakani da Allah ba, tilas ne kowanen mu ya daura aniyar fara gyara daga kansa. Akwai abubuwan da ba gwamnati ce ko Buhari ne zai zo ya gyara mana ba. Musamman yadda kowanen mu, yake gudanar da mu’amalarsa a tsakaninsa da iyalinsa da yadda yake yi da makwabtansa da mutanen unguwarsu da wuraren harkokinsa, ba Buhari ne zai tsaya a kansa ya ce ya yi abun da ya dace ba. Imaninsa da Allah da hukunce -hukuncensa zai yi amfani da su wajen yin abin da ya dace ko akasin haka, muyi ruko da igiyar Allah, mu daina rarrabuwa. mu kiyaye dokokinsa da umarninsa, mu yi abin da yace, mu bar abin da ya hane mu, shi ne zaman lafiyarmu, Allah ya tsara mana yadda zamu rayu da juna, komai irin bambancin da ke tsakaninmu, na addini, kabila, bangare, ko launin fata, illa mu bi wannan tsari da Allah ya shinfida mana.

Shugaban kasa Buhari hutu bai sameka ba Arewa tana neman durkushewa saboda rashin tsaro, ka dawo gida domin tunkarar abunda ke gabanka na kare lafiya da dukiyoyin al’umma, haka ministan tsaro kamar yadda ka bayyana cewar ana zargin wasu sarakunan gargajiya a Zamfara da saka hannun su a harkar ta’addanci, mu ‘yan Najeriya ba abun da muke bukata ka fadamana kenan ya kamata duk wanda aka ce ana zargi to a yi kwakwaran bincike idan yana da hannu a hakunta shi idan bashi da hannu a kyale shi.

Leave a Reply