A KIYAYE: ‘Yan Fashin Zamfara Da Katsina Sun Fara Sulalewa Kano, Kaduna Da Neja – Burutai

0
395

Daga Yaseer Kallah

Babban hafsan rundunar sojin kasa ta Nijeriya, Laftanal Janar Tukur Yusuf Burutai ya yi gargadi a kan yadda ‘yan fashin jihar Zamfara da Katsina ke sulalewa zuwa wasu jihohi kamar Kaduna, Kano da Neja.

Burutai, wanda ya yi jawabi a gurin wani taron manema labarai game da kara shirya rundunar harbin kunama da aka gabatar a shalkwatar soji da ke Habuja, ya ce ‘yan fashin sun fara arcewa daga Zamfara zuwa wadannan jihohin.

Burutai ya kara da fadin cewa ‘yan fashin na arcewa ne daga Zamfarar saboda nasarorin da rundunar sojin ke samu gurin yakar ta’addancin da ke hayyatar jihohin Zamfara da Katsina.

Ya kuma yi sanarwar cewa sojin za su gabatar da aiki na musamman a johohin da ‘yan fashin ke guduwa domin kare su daga kaidinsu da kuma dukkan sauran ayyukan laifi.

Leave a Reply