AZZALUMI MUGU ‘DAN TA’ADDA – INJI DATTI ASSALAFIY

0
791

Daga Datti Assalafiy 

Jama’a wannan mutumi da ake gani a hoto tsohon soja ne wanda aka koreshi daga aiki bisa aikata laifin fyade, sunansa Akhigbe Tijjani.

Sojan yana da aiki da shiyyar rundinar sojin hadin gwiwa na 27 a jihar Yobe, watarana sun fita duba gidajen mutane da ake zargin ‘yan ta’adda ne a wasu kauyuka dake jihar Yobe, sai shi wannan korarren sojan ya shiga wani gida inda ya tarar da wata budurwa tare da iyayenta, sai ya musu barazana kuma ya yiwa budurwan fyade a gaban ‘yan uwanta.

Bayan sojan ya kammala yiwa budurwan fyade, sai ya umarci yayan budurwan da cewa dole shima sai ya sadu da budurwan wato kanwarshi a gaban iyayen su, shine yayan budurwan yaki bin umarni sojan, daga nan sai sojan yayi amfani da wani abu mai tsini ya buga akan yayan budurwan da ya yiwa fyade.

Abokin aikin sojan ne ya kasa daurewa bisa wannan mugun aika-aika da korarren sojan ya aikata, shine abokin nasa ya kai rahoto gurin manyansu, bayan rundinar sojin Nigeria ta tabbatar da laifin sai ta koreshi daga aiki, sannan ta mikashi hannun ‘yan sandan jihar Yobe don a kammala bincike a gurfanar dashi a gaban alkali, kamar yadda mai magana da yawun rundinar ‘yan sandan jihar Yobe ASP Abdulmalik Abdulhafiz ya tabbatar.

Hakika wannan lamarin ya girgiza zuciyata, na kara tsanar wannan arne korarren soja azzalumi mugu ‘dan ta’adda, ana aikata irin wannan mugun zalunci da cin zarafi ta ina ne Allah Zai taimaki jami’an tsaro su samu cikakken nasara akan ‘yan ta’adda?

Yaa Allah Ka sa alkali ya daureshi har karshen rayuwarsa Amin.

Leave a Reply