HANYOYI BIYAR (5) DA ZA’A BI A MAGANCE MATSALAR TSARO A HANYAR KADUNA ZUWA ABUJA

0
460

Daga Datti Assalafiy

Tsohon babban sufeta janar na rundunar ‘yan sandan Nigeria IGP Mr Mike Okiro (rtd) yayi gamsasshen bayani akan hanyoyin da za’abi a magance barazanar barayi ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

-Hanyar na farko yace: Dole a samu cikakken hadin kai da goyon baya tsakanin dukkan hukumomin tsaron Nigeria da suke aiki a jihar Kaduna.

-Hanya na biyu yace: mutanen da suke aikata ta’addanci akan hanyar Kaduna zuwa Abuja suna nan a cikin jihar Kadunan, ba daga wani guri suke zuwa ba, dole a san motsi da zirga zirgansu, kuma ba zai taba yiwuwa ace jami’an tsaro da fararen hula basu san su ba, dole a samu hadin kai tsakanin jami’an tsaro da fararen hula ta yanda za’a bi diddiginsu ana kamasu.

-Hanya na uku yace: ‘yan sanda ba zasu iya magance matsalar ba har sai idan jama’ar wannan yanki da suke fama da barazanar tsaro sun basu cikakken hadin kai da sahihan bayanan sirri da kaiwa rahoton duk wanda basu yarda da take takensa ba ko an ganshi yazo a matsayin bako.

-Hanya na hudu yace: Gwamnatin Nigeria ta dauki nauyin horar da kwararrun jami’an tsaro akan abinda ya shafi yaki da masu garkuwa da mutane, sannan a wadata jami’an tsaro da kayan yaki wanda yafi na masu aikata laifin aminci da karfi da tasiri da illa.

-Hanya na biyar yace: Idan al’amarin tsaro ya lalace irin haka, to ya dace a koma kan tsarin da iyaye da kakanni suka bi wajen tabbatar da tsaro a lokacinsu, wato abinda ya shafi kafa kungiyoyin agaji na tsaro karkashin jagorancin malaman addini da shugabannin gargajiya tun daga kan unguwa, gudunma, yankuna, lardi, gari, kauyuka da birni, wannan zai bada dama a san duk wani bil’adama dake rayuwa a yankin kuma a san halinsa da sana’ar da yakeyi a fili ko a boye.

IGP Mike Okiro yace abin takaici ne yadda hanyar Abuja ta koma matattaran miyagun mutane masu satar mutane don neman kudin fansa, dole akwai wani boyayyen al’amari da yake faruwa, domin ba aljanu bane suke aikata mugun laifin mutane ne, kuma dole gwamnati ta dauki matakin gaggawa wajen magance matsalar.

Hakika wannan shawara tayi, Allah (T) muke roko Ya bawa shugabannin gwamnati damar yin amfani da wadannan gamsassun shawarwari Amin.

Leave a Reply