Hisbah Za Ta Fara Farautar Masu Cin Abinci A Bainar Jama’a Lokacin Azumi

0
149

Daga Yaseer Kallah

Babban kwamandan rundunar Hisbah ta jihar Kano, Malam Nabahani Usman, ya ce jami’ansa za su fara farautar baligan da ke cin abinci a bainar jama’a alhali ana cikin watan rahama na Ramadana.

Ya ce ba za su saki wadanda za su kama din ba sai idan mutum ya kawo sheda daga likita wadda ta nuna cewa ba zai iya azumi ba, ko kuma kuma ya nuna shedar yana da ciwon gyanbon ciki mai tsanani (Chronic Ulcer).

Kwamandan ya gaya wa BBC cewar idan mutum ya nuna shaidar to za su sake shi bayan sun ja masa kunne a kan kar ya kuma cin abinci a bainar jama’a alhali ana azumi.

Ya ce Ramadan wata ne mai girma ga Musulmai, sannan dukkan mabiyin addinin Musulunci dole ya azumci watan.

Leave a Reply