MAKIYA ZAMAN LAFIYAR NIGERIA NA KOKARIN KUNNA WUTAR RIKICI DOMIN SU HANA RANTSAR DA SHUGABA BUHARI – DATTI ASSALAFIY

0
1364

Daga Datti Assalafiy

Mai magana da yawun rundinar sojin Nigeria Kanar Sagir Musa ya bayyana cewa; wasu kasashen waje da wasu daidaikun mutane a Nigeria da wasu kungiyoyi masu zaman kansu suna cin amanar tsaron Nigeria ta hanyar assasa ayyukan ta’addanci da ayyukan ‘yan bindiga domin su hana rantsar da Buhari a matsayin shugaban Nigeria karo na biyu.

Rundinar sojin Nigeria ta kuma fahimci cewa wadannan makiya zaman lafiyar Nigeria da wasu kasashen waje suna tallafawa ayyukan kungiyar ISWAP/Boko Haram da wasu manyan kungiyoyin ‘yan bindiga da makudan kudi tare da basu goyon bayan da mafaka don su cigaba da haifar da barazanar tsaro a Nigeria.

Yanzu haka akwai wasu mutane suna alaka da kawance na kutu da kutu tsakaninsu da ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram don su karfafasu, wasu kuma suna yada bayanan karya da batanci akan hukumomin tsaron Nigeria domin su hada rikici tsakanin rundinar sojin Nigeria da ‘yan Nigeria da mahukuntan gwamnati, sannan mutanen suna sanyaya gwiwar dakarun sojin Nigeria da suke fagen daga ta hanyar fitar da labarun karya.

Irin wadannan miyagun mutane ne sukayi ta tsorata ‘yan Nigeria cewa zaben shekarar 2019 ba zai gudana ba, za’ayi tashin hankali, amma daga karshe sun kunyata anyi zabe lafiya, shiyasa yanzu suke bin hanyoyinsu wajen assasa wutar rikici da tallafawa ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga domin su tabbatar da cewa ba’a rantsar da shugaba Buhari ba zuwa karshen wannan wata.. kamar yadda kakakin rundinar sojin Nigeria Kanar Sagir Musa ya bayyana, mai beman karin bayani ya bincika jaridar Daily Trust na yau.

Muna rokon Allah Ya magance mana mutane da kasashen waje wadanda suke cin amanar tsaron Nigeria Amin.

Leave a Reply