An Kama Wani Dattijo Zai Tsallaka Kasar Saudiyya Da Miyagun Kwayoyi A Jihar Kano

0
200

Daga Jamilu Daya-malam Gama

Hukumar hana ta’ammuli da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA ta kama wani dattijo mai shekaru 72, Mai suna Mohammed Hamza da wani Kamisu Muhammad da haramtattun kwayoyi a filin tashi da saukan jirage ta Mallam Aminu Kano (MAKIA) a yayin da ya ke kokarin shiga jirgi zuwa kasar Saudiyya.

Kwamandan NDLEA na MAKIA, Mr Ambrose Umoru a yayin da ya ke yiwa manema labarai jawabi a jiya Jumu’a, ya ce an kama Hamza wanda dan asalin kauyen Gwaranduma ne a karamar hukumar Daura a jihar Katsina a lokacin da ake bincikar kayayakin matafiya.

Sai dai dattijon ya shaidawa jami’an NDLEA cewa ba shi da masaniya a kan yadda akayi kwayoyin suka shiga jakarsa.

“Mun gano cewa wasu ne da suka biya wa dattijon kudin jirgi zuwa kasar Saudiyya suka saka kwayoyin Tramadol a cikin jakar kayansa. Sun kawo shi Kano daga Katsina inda suka ajiye a Otel na kwanaki uku kuma a wannan lokacin ne suka saka kwayoyin jikin jakarsa ba tare da saninsa ba.

“A lokacin da jami’an mu suka gano muggan kwayoyin kuma ya fada mana inda ya fito. Ba tare da bata lokaci ba sai muka aike jami’an mu suka tsare Kamisu Mohammed.

“Kamar yadda bayannan mu suka nuna, an taba kama Mohammed da laifin saka muggan kwayoyi cikin jakkunan wasu mata biyu a baya. Sai dai a wancan lokacin matan tare suke aiki da Mohammed ba kamar dattijon nan da bai san hawa ba balle sauka,” inji Umoru.

Leave a Reply