ANNABI (S.A.W) YA CE AKWAI UQUBA GUDA BIYAR WANDA DUK MUSULMI SAI YA HADU DA ITA.

0
312

Daga Bashir Abdullahi El-Bash

1. Mutuwa da dacin fitan rai.
2. Kwanciyar kabari da duhun sa.
3. Tambayar kabari da tsananin sa.
4. Hawan siradi da santsin sa.
5. Awon mizani da qididdige shi.

SAI SAYYIDINA ABUBAKAR YA CE
YA RASULILLAH MINE NE ZAI IYA KAREMU DAGA WADANNAN
ABUBUWA GUDA BIYAR ?

SAI ANNABI (SAW) YA CE:
1. Sallar Asubah cikin jam’i yana hana jin dacin mutuwa.

2. Wanda ya yi sallar Azuhur
cikin jam’i za abuda kabarinsa da haske.

3. Wanda yayi sallar Asri cikin
jam’i za’a saukake masa tambayar
kabari.

4. Wanda ya yi sallar Magriba
za’a saukake masa hawan Siradi da santsin sa.

5. Wanda yayi sallar isha’i cikin
jam’i za’a saukake masa awon Mizani da qididdigeshi.

WANNAN SHINE KARIYAR DA ANNABI (SAW) YABAMU.

ALLAH YASA MU DACE DA RAHAMAR SA.

Allah Yabamu Albarkan Wannan Rana Ta Juma’a

Leave a Reply