Bayan da Marigayi Umaru Musa Yar’adua ya cika shekaru 9 da Rasuwa, Ga kadan daga cikin Takaitaccen Tarihin Rayuwarsa.

0
430

Daga Magaji Ontop Daura.

An haifi Alhaji Umaru Musa ‘Yar Adua ranar
16 ga watan Agustan shekarar 1951 a garin Katsina Mahaifinsa tsohon ministan Legas ne jamhuriya ta daya kuma matawallen Katsina,
sarautar da marigayi Alhaji UmaruMusa Yar
Adua ya gada. Ya shiga makarantar firamari ta Rafukka a shekarar 1958, kuma daga bisani aka mayar da shi makarantar Firamare ta kwana dake Dutsimma.

A shekarar 1965 zuwa 1969 ya yi kwalejin
gwamnati ta Keffi. Daga nan kuma ya tafi kwalejin Barewa, inda ya kammala a shekarar 1971. Ya shiga jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria a shekarar 1972 zuwa 1975, inda yayi karatun digirinsa na fannin ilimin koyarwa da na kimiyyar Sinadirai.

A shekarar 1978 ne ya koma jami’ar Ahmadu
Bellon domin yin digirinsa na biyu a fannin
ilimin kimiyyar sinadaren.
Aikin farko da Alhaji Umaru Musa ‘Yar Adua
ya fara shi ne na koyarwa a kwalejin Holy
Trinity dake Lagas a shekarar 1975zuwa 1976
kuma dagabisani ya koma koyarwa a kwalejin
kimiyya da fasaha dake Zaria a tsakanin
shekarun 1976 zuwa 1979 ya kuma ci gaba da
koyarwa a kwalejinshare fagen shiga jami’a
ta Zariya har zuwa 1983.

Daga nan ya yi aiki a wurare daban daban.
A lokacin jamhuriya ta biyu ‘Yaradua ya kasance dan jam’iyyar PRP yayin da a wannan lokacin mahaifinsa ne mataimakin shugaban jam’iyyar NPN na dan wani lokaci. A lokacin da janar Ibrahim Babangida ke shirin maida mulki ga hannun farar hula Umaru Musa ‘Yar Adua ya kasance daga cikin mutanan da suka kafa wata kungiya mai suna Peoples Front wadda wansa janar Shehu Musa Yar Adua ya jagoranta, kuma
itace ta rikide ta zama jam’iyyar SDP.

A shekarar 1991, Alhaji Umaru Musa ‘YarAdua ya tsaya takarar gwamnan jihar Katsina a karkashin jam’iyyar SDP inda ya sha kaye a hannun Sa’idu Barda na jam’iyyar NRC.
‘Yar Adua ya sake tsayawa takarar gwamnan
jahar Katsina a shekarar 1999 karkashin tutar
jam’iyyar PDP, inda ya yi nasara, an kuma
sake zabar sa a shekara ta 2003.

Alh. Umaru Musa Yar’adua ya kasance gwamna da shugaban kasa na farko a Najeriya da ya fara bayyana kadarorinsa, a wani matakin da wasu ke ganin na yaki da cin hanci da rashawa ne a tsakanin masu rike da mukaman gwamnati a Najeriya.

Allah ya yiwa Alhaji Umaru Musa ‘Yar Adua
rasuwa ranar 5 ga watan Mayun shekara ta
2010, alhalin yana Shugaban kasar Nigeria a sakamakon fama da yayi na Rashin Lafiya. Ya kuma rasu ya bar mace daya Hajiya Turai Yar Adua da ‘ya’ya bakwai biyar mata biyu maza.

Muna Addu’ar Allah ya Kyautata Makwancinsa, yasa Aljanna ce Makomarsa da mu Bakidaya Aamin.

Leave a Reply