DUNIYA KUNDI: Shin Kun San Motar Farko Da Aka Fara Kerawa, Ko Kun San Wanda Ya Kirkiri Mota?

0
340

Daga Haji Shehu

Shirin duniya kundi zai haska kadan daga cikin rayuwar Karl Benz Dan kasar Jamus da yafara kera motar hawa ta zamani a duniya.

Karl Friedrich Benz Dan kasar Jamus masani kuma fasihi a fannin kir-kirar Injuna da gyare-gyare shine mutum na farko da ya fara kera motar hawa ta zamani a shekarar 1885. Motar da ya kera ta ‘Benz MotorWargen’ ita ce motar hawa ta farko da aka fara sarrafawa a tarihin duniya.

Karbuwar fasahar kere-keren Karl Benz a duniya, ta sanya shi fadada harkokin shi kama daga sabuntawa zuwa kir-kirar wasu nauoin motati daidai da zamani. Karl Benz ya kirkiri Mototi kamar su ‘Velo’ (1894). Benz Viktoria (1894). Benz Omnibus (1895) da sauran su.

Karl Benz ya sha gwagwarmaya a fagen fasahar kere-keren Injuna da kuma gyaran su, ya shafe shekaru 84 a duniya. An haifi Karl Friedrich Benz a Mühlburg, Baden, dake Kasar Jamus cikin shekarar 1844. Ya mutu a Ladenburg, Baden, na kasar Jamus cikin shekarar 1929. Yanzu haka kabarin Karl Benz yana Makabartar Ladenburg dake Kasar Jamus.

Zaku iya aiko mana da tambayoyin ku ta wannan lambar 070 63177943, domin amsa muku ita cikin wannan Shiri dake zuwa muku duk karshen mako.

Leave a Reply