GUZURIN RAMADAN: Falala Ashirin (20) Na Watan Ramadan Da Kuma Abubuwan Dake Karya Azumi.

0
311

Tare Da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.

1, A CIKIN SA AKA SAUKAR DA ALKURANI MAI Girma. BAKARA 185
2, DUKKAN LITTAFAN ALLAH MAI GIRMA, A CIKIN SA AKA SAUKAR DA SU, TAKARDUN ANNABI IBRAHIM A DARAN FARKO NA WATAN, ATTAURAN ANNABI MUSA A RANAR 6 GA WATAN, INJILAR ANNABI ISA 13 GA WATAN, ALKUR’ANI ANNABI MUHAMMAD SAW , A RANAR 24 GA WATAN, MUSNAD AHMAD, SHAIK ALBANY YA INGANTASHI .
3, ANA BUDE KOFOFIN ALJANNAH A CIKIN WATAN,
4, ANA RUFE KOFOFIN WUTA
5, ANA DAURE KANGARARRUN SHEDANU
6, ANA BUDE KOFOFIN RAHMA
7, ANA BUDE KOFOFIN SAMA
8, MAI KIRA YANA KIRA, YA MAI NEMAN ALKHAIRI GABATO, YA MAI NEMAN SHARRI, KAYI NISA
9, A KO WANNE DARE, ALLAH YANA YANTA BAYI DAGA WUTA
10, A CIKIN WATAN AKWAI DARAN LAILATUL KADRI WANDA YAFI WATA DUBU,
11, ANA KANKARE ZUNUBIN SHEKARA, ANNABI SAW YACE, DAGA RAMADANA ZUWA RAMADAN AKA KANKARE ZANUBI DUKA, MUTUKAR AN NISANCIKABA’IRA
12, AN DURMUZA HANCIN, DUK WANDA RAMADANA YA KAMA HAR YA WUCE BAIYI AIKIN DA ZAAYI MASA RAHMA BA.
13, UMRA A CIKIN WATAN RAMADAN DAIDAI YAKE DA AIKIN HAJJI TARE DA ANNABI, SAW A WAJAN LADA.
14, WATAN DA AKAFI SHIGA I’ITIKAF, A GOMAN KARSHE
15, WATAN DA AKE AMSA ADDU’A
16, WATAN DA AKESON YAWAITA KARATUN ALKURANI MAI GIRMA , AKALLA SAUKA HUDU, DUK SATI DAYA.
17,WATAN ALKHAIRI da KYAUTA DA CIYARWA, DA SAMUN DUMBIN LADA, DUK WANDA YA CIYAR DA MAI AZUMI, ZAI KARA SAMUN LADA KAMAR YAYI AZUMI.
18, WATAN DA AKAFI YAWAN KIYAMUL LAIFI DA TARAWIH DA TAHUJJUD DA ASHAM, DON KARA KUSANCI DA ALLAH.
19, WATAN NEMAN NASARA AKAN MAKIYA.

ABUBUWAN DA SUKE KARYA AZUMI

NA DAYA: CIN ABINCI DA GANGAN,
NA BIYU: SHAN ABIN SHA DA GANGAN.
NA UKU : SADUWA DA MACE DA GANGAN.
NA HUDU: KAKARO AMAI DA GANGAN.
NA BIYAR: FASA NIYAR AZUMI.
NA SHIDA: RASHIN DAUKO NIYA TUN DARE GA MAI AZUMINSA FARILLA.
NA BAKWAI : ZUWAN JININ AL’ADA KO NA HAIHUWA ANA CIKIN AZUMI.
NA TAKWAS : SHAFAR GABA DA SHAAWA, KO KALLO, DA SHAAWA, KO TUNANIN MACE DA SHAAWA, HAR MANIYYI YA FITO.
NA TARA: YIN RIDDA DA FITA MUSULUNCI.

Leave a Reply