HALIN DA MUKA TSINCI KANMU YAU A NIGERIA INA MAFITA – DATTI ASSALAFIY

1
1054

Daga Datti Assalafiy

Dan uwa kayi kokarin karanta wannan jawabin har karshe, sannan ka yadashi zuwa ga inda ya dace, domin jawabine da ya fito daga bakin waliyin Allah, babban Malaminmu marigayi Sheikh Albaniy Zaria (RH) wanda ni Datti Assalafiy nayi aikin transcription din bayanin, bayan anyi zaben shekarar 2011 su Jonathan sunci zabe, sai a shekarar 2012 Malam Albaniy ya bada kyawawan shawarwari da hasashe masu gamsarwa ga ‘yan Nigeria domin samun mafita daga cikin matsalolin da suka addabemu, Malam Albaniy Zaria yace:

“..Kowa yasan ana zaune lafiya a Nigerian nan a lokacin da su Sardauna suka bayyana a matsayin shugabanni adilai, aka samu su Tafawa Balewa, aka samu su Awolowa, aka samu su Azikwe, kowa yana gwagwarmaya ne ya za’ayi ya ‘yanta mutanenshi, talakawan a lokacin dagaske suke.

Da aka fara samun gurbacewa daga talakawan, da Allah Ya tashi sai ya sallado Ya turo makiya sai sukabi dare daya sai suka kashe wadannan mutanen kirkin, hakane ko ba haka ba? haka ne, su da suka hau meye sukayi wa kasar wanda ya amfanar da ita a cikin watannin da sukayi?

Tundaga lokacin da su Aguiyi Ironsi suka kashe su Sardauna har zuwa yau an sake samun wani shugaba wanda akaji dadinshi? ba’a samu ba.
Wanda ya taho za’aji dadin nashi shima aka sake kashe shi Murtala Muhammad, wani ya sake tasowa za’aji dadinshi shine ‘Yar’adua shima ya mutu, Allah Yaki barwa kasar wanda zai rahamamata, me yasa? laifin shugabannin ne? eh!, laifin talakawan ne? eh!, domin daga cikin talakawan ne aka fitar da shugabannin, to in wani yazo mutumin kirki sai Allah Madaukakin Sarki yaga cewa bai dace dasu ba.

Wallahi in gaya muku sarahatan wadanda mukasha hira dasu nasha fada musu cewa; da talakawa suke cewa Nigeria sai maigaskiya suna nufin Buhari, sai nake cewa Buhari bai dace da yayi shugabancin kasarnan a irin wannan lokacin ba, domin suwa zai shugabanta? Suwaye zasu zama ministoci? Su wanene gwamnonin? Su wanene kwamishinonin? Su wanene campaign managers na Buharin?

Kudi akazo ana tarawa a cikin tim din campaign Buhari, campaign manager din ya kara naira miliyan sittin (60,000,000), naira miliyan sittin campaign manager na Buhari ya kara zai sace a cikin abinda ake nema, da aka zaunar dashi a gaban Buhari akace wadannan figures din fa? Sai yace a yafe mishi, yana da ‘ya’ya yana da mata bai san yadda zaiyi ba, shine da ya samu wannan damar shine ya ‘dan ‘kara, a cikin campaign team na Buhari, bana fa 2011 ‘din da ta wuce, ba wai shekara kaza ba, a wannan hayaniyar da kukayi tayi Nigeria sai maigaskiya, irin masu gaskiyar da suka kewaye Buharin kenan.
Sannan shi wancan da yaketa kwarmato jeka ka sameshi, me ake ciki dashi tun a wannan lokacin, zai yiwu mai gaskiya daya ya shugabanci kasa? Ba zai yiwu ba sai an samu masu gaskiya.

A lokacin da Tafawa Balewa yake shine prime minister na kasa gaba daya, Sardauna shine firimiyan arewa, mai gaskiya sama mai gaskiya kasa, a lokacin suma talakawan gaskiya suke so sai akaji dadi, amma kunsan yakai lokacin da talakawan suka lalace da sukaji an kashe Sardauna akwai wadanda suka zuba ruwa a kasa suka sha saboda dadi da murna? Yau wadannan mutane sunyi nadama ko basuyi nadama ba?

Saboda haka kuji jama’a; babu shakka tun daga sadda Buhari ya fara tsayawa takaran shugaban kasa kowa yasan karara nake fitowa nace indai maganar Buhari ne babu ja da baya muna tare dashi dari bisa dari (No compromise)

Don Girman Allah masu daukar wannan kasusuwana suna kaiwa Namadi Sambo ban yafe musu ba in basu kai wannan kaset din ba, kaje ka tambayi Namadi Sambo lokacin da za’ayi zaben shugaban kasa mun zauna dashi, yace Sabon-Gari da Zaria ta rikice, wani taimako zakayi mana Malam Albaniy Zaria?
Sai nace to indai maganar Buhari ne no compromise, sai yace Buhari ba zaici ba, sai nace a wurin Allah ne zaici, nace domin Rankayadade kai dinnan lokacin da ka fito takarar gwamna wace hanya mukabi jama’a suka yarda suka zabeka? Allah ne Ya kawo mana fasahar, a cikin kwana nawa mukayiwa Namadi campaign lokacin da ya fito takaran gwamna, campaign nawa mukayi? Amma dangwala kuri’ah jama’a sukayi sukace tunda Malam Albaniy Zaria yace a dangwala masa za’a dangwala.

Amma kasan har lokacin da ni kaina nace a zabeshi a matsayin gwamna sau daya na taba ganinshi? Kasan bayan yaci gwamna sai da ya shekara daya dundi sannan na samu damar yin magana dashi a waya ta hanyar matarshi? Ban taba buga mishi waya ya dauka ba, har shekara guda ban taba ganinshi ba, nace saboda haka maganar Buhari ba zaiyi shugaban kasa ba a hannun Allah ne, abinda Namadi Sambo ya gayan kenan Buhari dai bazaici ba, nace masa a hannun Allah ne.

Me yasa Buhari ya zamo musu tashin hankali?
Me yasa yanzu suke ta farfagandan cewa ai Buhari yace ba zai tsaya takara ba?
Me yasa suke ganin Buhari a matsayin barazana garesu idan zai fito takara a shekarar 2015?
Me yasa jiya tashar AIT da channel news, STV sukayiwa Buhari sharri cewa Buhari yace in kaza kaza kaza 2015 kaza kaza kaza a yaushe? ina?, a ina Buhari ya fadi wannan maganar?

Duk wannan suna ganin matsayin barazanace garesu, amma tare da haka kuji ku talakawa ‘yan uwana, ina fadin haka ina cewa Buhari bai dace ya zama shugaban kasar Nigeria ba, saboda ku talakawan baku dace da Buhari ya zama shugabanku ba, don in Buhari ya zama shugabanku hawan jini ne zai kamashi.

Daga cikin abinda ya kashe shugaba ‘Yar’adua shine hawan jini, abokina me bashi shawara na musamman akan harkokin shari’ah lauya ne, yace; lokacin da yaje ya samu shugaba ‘Yar’adua akan kudin wutar lantarki da aka cinye, yace; da ‘Yar’adua ya daga kai ya kalleshi sai ya sunkuyar da kai, yace sai ya dauka nazari ‘Yar’adua yakeyi irin na manya, sai ya bashi wuri, yace yana fita sai akace shugaba ‘Yar’adua ya suma, shine aka rahalashi akayi Saudiyyah dashi, dawowar da bai yita cikin lafiya ba kenan har ya mutu heart attack!, me yasa?

Saudiyyah ta baiwa Nigeria kyautar kayayyakin da za’a magance matsalar wutar lantarki dashi a Nigeria, Saudiyya ta bada kaza ta bada falwaya ta bada taransufoma, ta bada kaza ta bada kaza, sai akace wa shugaba ‘Yar’adua ga kaya sun tabbata, ya bada kudin aiki naira biliyan goma sha daya (11,000,000,000)ya dauka ya bayar, amma sai suka kasafta kudin tsakanin sanatoci da commissioners wadanda suke wakiltar zones da wasu manya suka raba kudin gaba daya, kayayyakin da Saudiyyah ta bayar kyauta duka suka cinye, da aka tura musu EFCC aka kama wasun su kwana nawa sukayi a gidan yari (prison)? kwana ashirin da takwas (28days) sukayi
Manyan sarakunan kasarmu na musulunci dake wakiltar ‘Dan Fodio su sukaje suka kama kafar Sarkin Katsina ya kama musu kafa akaje aka roki a sakosu, yaransu ne, shikenan, ta kare.
Ina wanda suka cinye kudin ‘yan sanda na fansho? an sakoshi yau kwana hudu, shikenan managa ta kare, yaransu ne.

A irin wannan halin ne Buhari zaizo ya zama shugaban kasa?
Da wa zaiyi aiki?
Wa zai zama masa minister?
Pastor Bakari da aka sashi kaje kaga irin corruption na pastor Bakari a cikin cocinshi, “innalLaha laa yugayyiru maa bi Qaumin hattaa yugayyiru maa bi anfusihim”.
Saboda haka in kuna so Nigeria sai maigaskiya ku fara zama masu gaskiya ku da kanku.
Kana da gaskiya tsakaninka da matarka? Kai shugaban kungiya mai gaskiya ne game da tsakaninka da mutanen kungiyarka? Kai Shehin Darika kana da gaskiya tsakaninka da muridanka? Kai me wa’azin masallaci kana da gaskiya tsakaninka da dalibanka.

Kowa yaje yayiwa kanshi bincike jama’a, “innalLaha laa yugayyiru ma bi Qaumin hattaa yugayyiru maa bi anfusihim”, shiyasa Allah Madaukakin Sarki ya zare wanda yafi dacewa da ‘yan Nigeria ya kakaba musu, ku kiyaye!
Allah Ya dauki (Jonathan) da ya dace da mutanen kasar ne ya basu, suna so basa so Allah Yayi Yayi ga abinda Yake so bazaku bi ba, don haka Zai cigaba da ‘daura muku irin wadanda suka dace daku.

Gashi karatune yake fadi yau shekara dari shida (600) da rubuta wannan littafin dake gabana yake cewa; “ayyukan bayi ne talakawa suke bayyanarwa wa talakawa a matsayin ainin shugabanninsu….”

Muna rokon Allah Ya karbi shahadar Malam Albaniy Zaria, Allah Ya jikan shugaba Umar Musa ‘Yar adua Amin

1 COMMENT

Leave a Reply