KALAMAN MALAM ALBANIY ZARIA AKAN SHUGABA UMAR MUSA ‘YAR ADUWA – DATTI ASSALAFIY

0
434

Daga Datti Assalafiy

A yau ne Lahadi 5-5-2019 tsohon shugaban Kasarmu Nigeria Marigayi Alhaji Umaru Musa ‘Yar adua ya cika shekaru 9 da rasuwa bayan yayi shekaru 2 akan kujerar shugabancin Nigeria, ganin yadda ake tunawa da mutuwarsa sai ya tunatar dani wasu magangu da Marigayi Malam Albaniy Zaria ya fadi a kanshi, hakika Umar Muda Yar’adua mutumin kirki ne mai son gaskiya.

Amma maciya amanar lokacinsa suka cutar dashi, kamar yadda maciyar da suke gewaye da shugaba Buhari a yanzu suke cin amanarsa suka hanashi yin abinda ya dace.

A shekarar 20011 Marigayi Sheikh Albaniy Zaria yace: “A shekarar 2007 sai da shugaba Umar Musa ‘Yar adua yace wa mukarrabansa ku rufa min asiri in sauka, saboda ya gano cewa bashi ya lashe zaben shugaban kasa ba, Buhari ne ya lashe zaben, mukarrabanshi sukace ba zamu yarda ka sauka ba.

An fito da gaskiya yaga cewa ya fadi zabe sai yace wa mukarrabansa ku taimakeni don Allah in sauka, sukace ah’ah!, idan ka sauka mu muna so, to kuma tunda kaine a kai dole ka zauna don mu.

Na daga cikin abinda ya karawa bawan Allah nan hawan-jini da bala’o’in da mukarrabanshi suka sakashi a ciki, saboda su suke cin moriyar abin.

Akazo Alkalai suka tabbatar da cewa gaskiye ne ‘Yar adua bai ci zaben 2007 ba, to sai akace ayi amfani da wata ka’ida “Hukumul hakimu yarfa’ul khilaf”,akwai wannan ka’idar a kowani irin dokokin shari’ah (Law), akwai a “Civil Law”, “Canon Law” da sauransu, ma’ana wato idan Alkalai sukayi sabani a yanke hukunci, sai ace abinda babbansu ya hukunta shikenan.

Kawai sai babban lauyan Nigeria na lokacin ya hukunta cewa ba za’a bawa shugaba Buhari kujeran shugabancin Nigeria ba, amma a shari’ance an tabbatar shi yaci zaben 2007, to wadannan shine irin kotunan da muke dasu a Nigeria…” ~Marigayi Sheikh Muhammad Auwal Adam Albaniy Zaria.

Shugaba Umar ‘Yar adua ya assasa abubuwa masu girma na alheri domin amfanar ‘yan Nigeria, misali da tashar jiragen ruwa na arewa da za’a gina a jihar Niger, amma bayan ta Allah ta kasance a kanshi (mutuwa) Jonathan yana zuwa sai ya dakatar da wadannan abubuwa saboda mugunta.

A lokacinsa ne gwamnatin Saudiyyah ta taimakawa gwamnatin Nigeria da tallafi na dukkan kayayyakin da za’a gyara matsalar wutar lantarki a Nigeria, kawai gwamnatin Nigeria zata biya kudin saka kayayyakin ne, aka yiwa shugaba Umar ‘Yar adua bill cewa za’a kashe kudi kimanin Naira biliyoyin 11, kuma ya amince aka fitar da kudin, amma wasu azzalumai mukarrabansa suka batar da kudin da kuma kayayyakin da Saudiyyah ta bayar har zuwa yau, da akazo aka fadawa ‘Yar adua cewa an cinye kudin, nan take ya fadi ya suma, aka fita dashi Kasar Saudiyyah, kwanansa ya kare a can.

A lokacin ne EFCC ta dira kan manyan permanent secretaries na ma’aikatan wutar lantarki na kasa, aka kama wasu, daga bisani labarin binciken yabi iska duk aka sako su, wannan itace Kasarmu Nigeria!.

Allah Ka jikan shugaba Umaru Musa ‘Yar adua Ka yafe masa kura-kurai Ka saka masa da Aljannah Amin.

Leave a Reply