RUNDINAR SOJIN NIGERIA TA HARAMTA HAWA BABURA A GURAREN DA AKE FAMA DA MATSALAR GARKUWA DA MUTANE – DATTI ASSALAFIY

0
1392

Daga Datti Assalafiy

Rundinar sojin Nigeria ta fitar da sanarwan hana hawa babura a guraren da ake fama da masifar garkuwa da mutane a tsakanin jihohin Zamfara, Kebbi, Katsina, Sokoto, Kano, Kaduna da kuma jihar Niger.

Wannan sanarwan ya fito ne daga Mai magana da yawun rundinar sojin Nigeria Kanar Sagir Musa, yace rundinar Operation Harbin Kunama ta lura cewa masu aikata laifukan yin garkuwa da mutane a wadannan johohi guda shida, suna yin amfani da babura ne wajen aikata mugun laifinsu su gudu cikin dazuka, daukar matakin haramta hawa babura a guraren da ake fama da matsalar yana da nasaba wajen inganta tsaron yanki.

Kakakin rundinar sojin yaci gaba da cewa, wannan matakin da rundinar soji ta dauka babu shakka zai shafi fararen hula, amma suyi hakuri, dole ce tasa a dauki dukkan matakin da ya dace wajen kawo karshen masu aikata miyagun laifuka ta kowace hanya.

Don haka rundinar sojin tana kira ga jama’ar yankin da abin ya shafa su bada hadin kai, an haramta hawa babura daga yau, duk yankuna da dazukan da rundinar Operation Harbin Kunama ta mamaye aka kuskura aka ga wani akan babur, to rundinar zata daukeshi a matsayin ‘dan bindiga ko kuma mai garkuwa da mutane, don haka a kiyaye, wannan matakin ya shafi iya yankunan da ake fama da matsalolin garkuwa da mutanene a jihohin, Zamfara, Kebbi, Sokoto, Katsina, Kano, Kaduna da Niger gurin da rundinar Operation Harbin Kunama ta mamaye.

Kakakin rundinar sojin Nigeria ya bukaci jama’a su taimaka wajen yada wannan sanarwan.
Muna rokon Allah Ya sa wannan mataki ya zama sanadin kawo karshen masu garkuwa da mutane Amin.

Leave a Reply