WATA SABUWA: Wajibi ne mu hukunta duk wanda keda hannu cikin cuwa-cuwar jarrabawar Jamb, Inji Shugaban hukumar Jamb.

0
255

Daga Haji Shehu

Hukumar jarrabawar share fagen shiga Jami’a (JAMB) ta soke wasu cibiyoyin gudanar da jarrbawa guda 76, hukumar ta kuma nada wani babban lauya (SAN) domin gurfanar da mutane 100 da ake zargi da cuwa-cuwar jarrabawa.

Kamar yadda shugaban hukumar ya baiyana, Na’urar daukar hoto ta CCTV da suka dasa a cikin cibiyoyin jarrbawar ta nadi faya-fayen Bidiyon yadda akayita musayar asalin masu rubuta jarrbawar da kuma wasu kwararru, Na’urar ta nadi yadda masu rubuta jarrabawar ke musanya kansu da wasu mutane a bandaki yayin rubuta jarrabawar ta Jamb.

A cewar shi sun gano mutane da dama wadanda suke shiga bandaki da zummar yin Uzuri amma daga bisani sai kaga wanda ya shiga bandakin ba shi yake fitowa ba, ya musanya kansa da wani wanda ya labe a bandakin domin rubuta masa jarrabawar.

Shugaban hukumar yace sun sanya Na’urar ne a sirrance cikin cibiyoyin jarrabawar domin Nadar abunda yafaru yayin zana jarrabawar.

Leave a Reply