YADDA ‘YAN MAJALISSAR DOKOKIN JIHAR KANO KE NEMAN HADDASA RABUWAR KAI TSAKANIN GWAMNA DA SARKI:-

0
318

Kamar yadda jama’a su ka sani, majalissar dokokin Jihar Kano, ta Na tattauna wani kuduri kan yadda za a datsa masarautar Kano zuwa masarautu biyar wadanda za su hada da: Gaya, Bichi, Karaye, Rano, da kuma Kano.

Ko kuma in ce a dawo musu da martabarsu Kamar yadda dama can akwai masarautun.

Kuma tuni har ma ta kafa wani kwamiti kan hakan.

Wannan kuduri, ya haifar da cece-kuce kala-kala har ma wasu Na zargin mai girma gwamna da hannu cikin batun.

Ana tsaka da wannan ne kuma sai aka samu wasu bayanan da su ke nuni da yadda hukumar yaki da rashawa da karbar korafe-korafe ta Jihar Kano ta fidda wasu bayanai ko wata takarda kan tuhuma ga mai Martaba sarkin kano ko fadar Kano alhalin kuwa shi shugaban hukumar Malam Muhyi Magaji ba ma ya ‘kasar.

Kenan wadannan batutuwa na da alamomin tambaya Kamar haka: wa ya saki wadancan bayanai, kuma wacce manufa ake son cimmawa ? Wadannan tambayoyi Na bukatar amsa.

In jama’a ba su manta ba, a baya ma wannan majalissar a ‘karkashin shugabanta da kuma shugaban masu rinjaye, Babba Dan Agundi shi Ne dai aka dakatar daga mukaminsa saboda zargin karbar nagoro daga wajen fitaccen Dan kasuwar nan, Alhaji Aliko Dangote domin majalissar ta janye tuhumar da su ke yi wa fadar sarkin na Kano. Kafin yanzu kuma ya dawo kan mukamansa.

Kenan a Iya cewa wannan kura da ta taso, akwai wasu daga cikin yan majalissar da su ke neman haddasa rudani da rashin fahimta a tsakanin mai girma gwamna da mai martaba Sarki.

Kuma jama’a ka da su manta, nan da ‘yan kwanaki Kadan wadannan Shugabannin majalissar za su tafi, to me kuma su ke son haddasawa su tafi su bari ? Ko shakka babu a Iya cewa su Na da wata boyayyiyar manufa kuma ya kamata asani kafin su tafi ?

Amma dai ko kadan wannan batu ba shi da wata Alaka da mai girma gwamna Dr. Abduallahi Umar Ganduje. Ba shi da hannu akai.

Sannan kuma, ya kamata jama’a su gane, ba shakka a baya an samu sabani tsakanin mai girma gwamna da mai martaba sarki, amma cikin ikon Allah an samu daidaito da masalaha, babu wata rashin jituwa yanzu a tsakaninsu.

Domin kuwa ko a baya-bayannan, mai girma gwamna Ne ya ba wa mai martaba damar aurar da zawarawan da gwamnatin kano ta aurar.

Dan haka, jama’a su yi watsi da duk wata jita-jita da ake yadawa kan Neman jinginawa mai girma gwamna laifi, ko Kadan me girma gwamna ba shi da hannu a ciki, kuma ya Na da kykkyawar fahimta da mai martaba.

Leave a Reply