FARIN JININ SHUGABA BUHARI YA RAGU SOSAI

0
186

Daga Datti Assalafiy

Babu shakka duk wani masoyin shugaba Buhari na gaske ba masoyin bogi ba yasan cewa farin jinin shugaba Buhari ya ragu matuka sosai, saboda yadda talakawa suke shan wahala suke korafi tare da dandana kudarsu a hannun masu garkuwa da mutane ba tare da an share musu hawaye ba.

Bayannan gashi Musulmai sun fara azumin watan ramadan gwamnatocin jihohin tarayyar Nigeria basu samu damar biyan albashi na watan da ya gabata ba, kuma ance tsaikon da aka samu daga gwamnatin tarayya ne, ni dai duk inda wata munasaba ta hadani da mutane shugaba Buhari suke jinginawa laifi kai tsaye.

Duk yadda za’a yi bai kamata gwamnati tayi sakaci wajen biyan ma’aikata albashi ba, musamman lura da cewa mafi rinjayen al’ummar Kasar musulmai ne da suke bukatar kudin da zasu sayawa iyalansu abincin da zasu ci a azumi, amma mahukunta sun hana, sun manta cewa addu’ar mai azumi a bakinsa karbabbiyace.

Bamu sani ba ko maciya amanar shugaba Buhari ne suka shirya manakisa domin su haddasa gaba da kiyayya tsakaninsa da talakawan Nigeria?

Wannan abin ya kara ragewa shugaba Buhari farin jini sosai, ba shugaba Buhari nake jiyewa illar hakan ba, mutanen da suke so su gaji shugaba Buhari bayan ya kammala wa’adin mulkinsa sune abin tausayi, da wahala su sake samun goyon baya daga talakawan arewa.

Muna rokon Allah Ya sasanta tsakanin shugaba Buhari da talakawan Nigeria, sannan muna rokon Allah Ya raba tsakanin shugaba Buhari da maciya amana.

Leave a Reply