ALLAH MADAUKAKIN SARKI SHINE KADAI BAI CANCANTA A MASA KISHIYA BA (SWT) – DATTI ASSALAFIY

0
317

Daga Datti Assalafiy

Tarihi ya nuna cewa ba tun yanzu bane aka gabatar da kuduri na kara yawan Sarakunan gargajiya masu mukamin Sarkin Yanka a jihar Kano, ance tun zamanin Abubakar Rimi, ita gwamnatin Maigirma Khadimul Islam Dr Abdullahi Umar Ganduje ta karasa abinda aka assasa ne.

Sannan girman Kano da yawan al’ummarta; ni a nawa fahimtar kamar an ragewa Mai martaba Sarki Malam Muhammadu Sunusi II nauyin shugabanci ne, da nauyin tambayoyin da zai amsa ranar da Allah Madaukakin Sarki Zai titsiyeshi da jama’ar Kano don yin Hisabi, a wannan ranar ce zaiyi danasin cewa da ma bai zama Sarki ba, masu ganin an tauye masa martaba a ranar Hisabi ba zaku iya amfana masa da komai ba, baram-baram zakuyi.

Har Kanawa kun manta lokacin da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana gwamna yayi watsi da ‘ya’yan tsohon Sarki marigayi Ado Bayero ya zabi Sunusi Lamido Sunusi don ya bakantawa Jonathan rai saboda siyasa?, har yau ban manta da irin mummunan zanga-zangar da akayi a Kano a lokacin ba, har kone konen kayan gwamnati sai da akayi, akace ba’a son Sunusi Lamido Sunusi, wasu suka dinga yayata cewa ‘dan shi’ah ne, aka dinga fitar da hotuna na batanci a kanshi.

Wasu saboda rashin adalci suna zargin cewa abinda aka yiwa Mai martaba Sarkin Kano siyasa ce, to amma sun manta cewa shima siyasace ta kawoshi, kuma sai yayi kuskuren shiga cikin siyasa ya nuna goyon bayansa a bangare guda daya yana yin fito na fito da gwamnatin tarayya da kuma gwamnatin jiha na Demokaradiyyah, hakan da yayi kuskure ne, tunda shi Sarki ne, kowa nashi ne.

Sannan da aka kara Sarakunan Yanka guda 4 a Kano duk da haka dole su kasance a karkashin umarni da ikon Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi, ya sake samun karin girma ne na zama sabon shugaban majalisar Sarakunan Yanka na jihar Kano, masu cewa kishiyoyi aka masa basu gane ya abin yake bane, kuma ai ALLAH MADAUKAKIN SARKI ne Kadai bai cancanta a masa kishiya ba (SWT).

Hakan da akayi ba zai rage masa albashi ba, ba kuma zai rage masa kima da daraja ba musamman idan ya rike mutuncin kanshi, sannan an yiwa tsatson zuriyar gidan tsohon Sarki Ado Bayero adalci ne, tunda ance akwai ‘dan sa da ya samu wannan karin girma da akayi.

Akwai jihohin Arewa da dama wadanda suke da Sarkin Yanka fiye da daya, kamar a jihar Bauchi muna da Sarakunan Yanka har guda 6 karkashin jagorancin Magajin Yakubun Bauchi Sarki Lirwanu Sulaimanu Adamu, jihar Borno wacce tsohuwar Masarauta ce da musulunci ya kafa kusan shekaru dubu, suma suna da Sarakunan Yanka karkashin jagorancin Shehun Borno Sarki Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi.

Tsarin dokar Kasar Nigeria ya bawa gwamna dama da karfin iko ya kori Sarkin Yanka daga kujerar Sarauta ma gaba daya, shugaban karamar hukuma (Chairman) yafi babban Sarkin Yanka daraja a tsarin Constitution, tuntuni an karya darajar Sarakunan Gargajiya tun lokacin da turawan mulkin mallaka suka mamaye yankin mu, dole Sarakunan Gargajiya su yiwa shugabannin gwamnatin Demokaradiyyah biyayya.

Don haka babu kuskure cikin abinda gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje tayi na kara yawan Sarakunan Yanka a jihar Kano, hakan da akayi daidai ne, daukaka darajar Kano ne, kuma adalci ne a tsakanin gidan masu sarauta biyu a Kano.

Muna rokon Allah Ya karawa jihar Kano albarka, Allah Ya taimaki gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje Ya bashi ikon sauke nauyin shugabancinsa Amin.

Leave a Reply