” In Zaka Fadi, Fadi Gaskiya. Komai ta jawo Maka Ka Biya”.

0
309

Daga Bashir Abdullahi El-bash

Da wani bangare na PRP ( ‘yan santsi) suka koma NPP, sai Shugaban NPP na kasa ya kawo ziyara lacca Kano. To da azumi ne. Aka shirya gawurtacciyar lacca a Wudil. Shugaba ya hau yana magana da turanci, ana fassarawa.

Can sai ya ce a cikin turancin, ‘…..kuma wannan azumi da ku ke shan wahalar yin kwana 30, to na yi maku alkawari, in mun ci zabe za mu maida shi kwana 3’. Nan da nan sai Shugaban ‘yan santsi ya cewa mai fassara: ‘kar ka fassara wannan! Ya dubi Shugaban NPP, ya ce da Hausa, ka ga mashirmaci, zai jawo mana masifa! Wani ya ce, Ai ranka ya dade, ya dauka sarakuna ne suke samu azumin tilas. Shugaban ‘yan santsi yana shafe gumi ya ce, A a! Amma fa ya so ya gama da mu. Tir.

Haka kuma da aka je Falgore, a irin wannan lacca da wannan bangare na PRP, ko in ce NPP, ya shirya, sai aka kira Shugaban Jam’iyya don ya yi magana. To Bafillatani ne domin Falgore kasar fulani ce.

Ya hau ya ce: N- fi – fi, N – fi – fi. Ya juyo, yana kada kai, ya ce, ‘ku sauko da shege ‘. Wani daga cikin wadanda suka je Wudil ya tambaye shi, ‘Ranka ya dade, a ina kake ne? ‘ Ya ce ‘Wallahi a gaskiya abin da daure kai.

Leave a Reply